Ambaliyar ruwa ta shafi mutum miliyan shida a Gabashin Afrika

Man wading through floodwater

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yankunan sun fuskanci damuna irinta da aka samu ruwan sama mafi yawa a cikin ƙarni

Adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa ya ruɓanya sau biyar a cikin shekara hudu a kasashen gabashin Afirka, a cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya.

Kusan mutane miliyan shida ambaliyar ta shafa a wannan shekarar inda tilastawa miliyan 1.5 barin matsugunansu.

Yankunan sun fuskanci damuna irinta da aka samu ruwan sama mafi yawa a cikin ƙarni.

A shekarar 2019, an zargi ƙaruwar ɗumamar yanayin da ta taso daga Tekun Indiya da haddasa ruwan saman kamar da bakin ƙwarya.

Bayanan da sashin jin-kai MDD ya fitar na tattare da damuwa kan irin asara da halin da ambaliyar ta jefa mutane.

Mutanen da ambaliyar ta shafa a Gabashin Afirka sun ƙaru zuwa miliyan huɗu a 2019 daga miliyan 1.1 a 2016, yayin da ta shafi kusan miliyan shida a wannan shekarar - wannan kuwa tun kafin a shiga lokacin marka-marka, da galibi ke somawa daga watan Nuwamba kuma ke shafar kasashe da dama a yankin.

1px transparent line

A Sudan daya daga cikin yankunan da ambaliyar ta fi shafa, gidajen mutane 860,000 sun lalace ko rushe, sannan sama da 120,000 sun rasa rayukansu, a cewar alƙaluman MDD.

Kusan kowacce jiha ta Sudan an tafka musu ruwa da ya haifar da ambaliya da makwabciyar kasar ta Sudan Ta Kudu, mutum 800,000 ambaliyar ta shafa, akwai kuma mutum 368,000 da suka rasa muhallansu.

Home submerged by water

Asalin hoton, UN-IOM

Bayanan hoto, Ambaliyar ta shafe wurare da dama a Sudan Ta Kudan

"Dukkanin mazaunan yankunan sun tsere zuwa wuri mai tudu domin tsira daga malalar ruwa," a cewar sanarwar MDD.

Bayan ziyartar yankunan da ambaliyar ta fi muni a Sudan Ta Kudu a watan da ya gabata, shugaban sashen jin-kai na MDD a kasar, Alain Noudéhou, ya ce "yanki mai girma da ke kusa da Tekun Nile yanzu ya nutse karkashin ruwa."

Yawan waɗanda ambaliya ta shafa . 2020. Number affected by flooding in 2020 .
1px transparent line

A Habasha, da yake da al'umma mafi yawa, mutane miliyan 1.1 ambaliyar ta sha.

Burundi da Djibouti da Kenya da Rwanda da Somalia da Tanzania da Uganda duk sun fuskanci irin wannan amabaliyar fa.