Ambaliyar ruwa a Sudan: Yadda sauyin yanayi zai rusa wuraren tarihin Afirka

A girl walks on sandbags along a flooded street in Sudan's capital Khartoum, 31 August 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sudan na fama da ambaliyar ruwa bayan Kogin Nilu ya yi tumbatsar da bai taba yi ba cvikin shekaru aru-aru

Tun daga zane-zanen dutse da ke Kudancin Afirka zuwa Dalar da ke gefen Kogin Nilu, al'umar da suka gabata sun bar tarihi a yankin Afirka.

Sai dai yanayi mai tsananin gaske da tumbatsar teku da sauran ƙalubale da ke da alaƙa da ɗumamar yanayi na barazanar lalata muhimman al'adun Afirka kamar yadda wani bincike ya yi gargaɗi.

Wasu masu bincike daga Burtaniya da Kenya da Amurka sun ce "za a rasa wasu daga cikin mahimman abubuwan tarihi na Afirka sakamakon sauyin yanayi cikin gomman shekaru matukar ba a yi wani abu a kai ba."

Gargaɗin na zuwa ne yayin da masu binciken kayan tarihi a Sudan ke ƙoƙarin hana ruwa daga kogin Nilu isa wurin kayan tarihin duniya da ke al-Bajrawiya.

Meroe pyramids at the UN-designated World Heritage Site at al-Bajrawiya in Sudan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dalollin al-Bajrawiya na da tarihin shekara 2,300

Wajen da ya taɓa zama birnin sarauta mai daula na tsohuwar daular Meroitic da ta shekara dubu biyu yana da ɗaruruwan kayayyakin tarihi.

Duk da ambaliya na faruwa a kogin Nilu duk shekara, mazauna wajen sun ce a wannan shekarar lamarin ya fi tsananta, ta kashe kusan mutum 100 tare da ɗaiɗaita wasu 500,000.

Wasu masana kimiyya sun ɗora laifin kan sauyin yanayi da bunƙasar birane a bakin kogin.

Nahiyar Afirka na da wuraren tarihi da Unesco ta lissafa, idan aka haɗa da waɗanda suke tsibiri waɗanda suke wani ɓangare na ƙasashen Turai.

Ga yadda sauyin yanayi ya shafi wasu daga cikin muhimman wuraren tarihin.

Sabratha, Libya

The UN designated site at Sabratha, on the Lybian coast

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sabratha tsohon wurin kasuwanci ne wanda ya shahara a karni na biyar

Wasu manyan wuraren tarihi biyar a Libya na cikin haɗari saboda ɓarnar da rikici ya haifar a ƙasar.

Daga cikin su akwai birnin Phoenician na Sabratha wanda ya taka muhimmiyar rawa a cinikayya tsakanin Afirka da tekun Bahar Rum.

Sabratha na daga cikin yankin Numidia da ke Massinissa kafin a haɗe da daular Romea kuma sake gina ta a ƙarni na 2 da na 3 AD.

The Roman theatre at Sabratha, Libya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu daga cikin abubuwan da Sabratha ke alfahari da su shi ne gidajen wasanni kwaikwayo irin na Romawa a Afirka

A yanzu, bincike ya nuna cewa zaizayar teku da tumbatsar teku da guguwa sun shafi Sabratha sosai.

Tashar ruwa da ke Suakin

Tashar ruwa da ke tsibirin Suakin, a arewa maso yammacin Sudan, ta taɓa zama tashar da ke da matukar muhimmanci a Bahar Maliya.

The town gate at the Red Sea port of Suakin in Sudan

Asalin hoton, Getty Images

Labarinta ya soma ne tun shekara 3,000 da ta gabata lokacin da sarakunan Masar suka mayar da tashar zuwa wajen kasuwanci da haƙe-haƙe.

A tsawon tarihi, Suakin ya zama wata matattarar mahajjata da ke kan hanyar zuwa Makkah sannan ya taka muhimmiyar rawa a cinikin bayi a Bahar Maliya.

Ya kuma taɓa zama wani ɓangare na Daular Ottoman.

Suakin in 1930

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan hoton, wanda aka dauka a 1930, yana nuna irin tarihin Suakin

Sai dai wajen ya lalace tun da ya rasa martabarsa shekara 100 da ta gabata. A yanzu, wajen na ɗauke da wasu kyawawan misalai na gidaje da masallatai a cewar Unesco.

A halin yanzu, Farfesa Clarke na gudanar da bincke don tantance yadda asarar ta kasance sakamakon cikar teku da kuma zaizayar teku.

"Abin da muka sani shi ne a 'yan shekaru masu zuwa lamarin zai shafi Bahar Maliya abin da ke nufin za a rasa shi matuƙar ba kai ɗauki ba]."

A shekarar 2018, Sudan da Turkiyya sun rattaba hannu kan kwantiragin shekara 99 na sake ƙawata Suakin amma masu suka a Turkiyya suna zargin akwai wani buri na daban.

Tsohon Garin Lamu, Kenya

The fort walls, 1813-1821, in Lamu Old Town (UNESCO World Heritage List, 2001)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi amannar cewa Lamu shi ne gari mafi tsufa a Kenya

Yankin Lamu Old shi ne matsugunin Swahili mafi tsufa a gabashin Afirka a cewar Unesco.

Saɓanin sauran ƙuyuka da aka yi watsi da su a gaɓr gabashin Afirka, jama'a sun ci gaba da zama a Lamu sama da shekara 700.

Majalisar Dinkin Duniya ta ƙara cewa wajen ya zama wata cibiya mai mahimmanci ta nazarin musulunci da al'adun Swahili.

An aerial view of Lamu Old Town in Kenya

Asalin hoton, National Museums of Kenya

Sai dai Lamu ta sha fuskantar koma-baya, ma'ana ta rasa kariya daga kasa da kuma itace.

"Wannan yana da nasaba da ginin tashar ruwan Lamu, wanda ke lallata dajin mangrove da ke kare tsibirin daga ambaliya," in ji Farfesa Clarke.

"Don haka yawancin abin da za mu kira kayan gado suna kariya ne ga al'adun gargajiyar. Kuma yayin da muke lalata al'adun gargajiyar, muna kuma yi wa wuraren al'adun gargajiyar illa."

Yankunan teku, Tsibirin Comoros

The city of Domoni on the west coast of Anjouan island, which is part of the Union of the Comoros

Asalin hoton, Getty Images

Gamayyar tsibirai da ake kira The Union of Comoros da ke kan gabar tekun gabashin Afirka a mashigin Mozambique, ba shi da Tarihi a Duniya, amma guda hudu kasar ke son mamayewa.

Yana da wata ingantacciyar fada ta karni na 13 da kuma sauran gine-ginen tun a karni na 16.

A woman is pictures in the medina of Mutsamudu, the capital of Anjouan Island, Comoros, March 2019

Asalin hoton, Getty Images

Amma Comoros tana daga cikin wurare "da suka fi fuskantar barazana" daga tumbatsar teku, a cewar Farfesa Clarke.

A wani yanayi na matsakaiciyar iska mai guba, "muhimman sassa na yankin a gabar teku na Afirka za su shafe zuwa 2100", a cewar wani sabon bincike.

"Daga 2050, Guinea, Gambia, Najeriya, Togo, Benin, Congo, Tunisia, Tanzaniya (hadi da Zanzibar) da kuma Comoros za su kasance cikin barazanar zaizaya da tumbatsar teku."

Tasoshin ruwa, Ghana

Artillery battery at Cape Coast castle, Ghana

Asalin hoton, Getty Images

Tekun Ghana yana cike da wuraren kasuwanci masu karfi da ginin zamanin da, wadanda suka kafu tsakanin 1482 da 1786, ds ke da girman kilomita 500 tsakanin Keta da Beyin.

Yan kasuwa daga kasashenPortugal da Spain da Denmark da Sweden da Holland da Jamus da kuma Birtaniya ne suke zaune a gidajen na Ghana.Gine-ginen sun taka rawa a kasuwancin zinari har zuwa lokacin cinikin bayi tsakani tsakanin Afrika da Amurka.

Aerial view of Fort Williams, Anomabu, Ghana

Asalin hoton, Getty Images

Amma gine ginen suna wurare ne da ke da cunkosun jama'a wanda matsalar sauyin yanayi ke yi wa barazana (kamar goguwa da tumbatsar teku.Farfesa Clarke ta ce misalan ire iren wadannan gine ginen kamar na Prinzenstein a Keta "teku ta shafe su.""Muna da hotuna na 1970 kuma muna da na yanzu, duka wurin ya shafe," kamar yadda ta shaida wa BBC.

Tsohon garin Djenné a Mali

Gidajen laka 2,000 a Djenne suna cikin hotuna kyawawa a Mali da suka samo asali tun 250 kafin haihuwar Annabi Isa..Djenne garin kasuwanci ne kuma mahadar cinikin zinari a tsakanin kasashen da ke sahara.A wajajen karni ma 15 zuwa 16 ya kasance cibiya ta yada addinin islama.

Houses in Djenné

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mazauna wanna yanki sun dogara ne da kayayyaki masu araha wajen sabunta gine-ginensu

"Wurare masu ban mamaki ''

Barazana ga al'adun Afirka ba game da sauyin yanayi ba ne kawai, har ma da ikon kasashe na rage tasirinsa.

Rock paintings depicting hunters, long-horned cattle and antelope, giraffes and elephants decorate granite caves in Laas Geel, Somalia. Pictured in June 2017

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutu a kusa da wani dutse da aka yi zanen da aka ce ya shekara 5,000 a kansa

Akwai kasashe kamar Masar, da ke zaune a wani yanayi mai 'babban hatsari na ambaliyar ruwa a cikin shekaru masu zuwa' amma kuma a shirye take ta tunkari wasu kalubale. Kasa kamar Somalia da ke fama da yaki hakan ya hana bayyana wasu wurarenta cikin wuraren tarihi na duniya.

A tarihance, mun san akwai wurare da yawa na tarihi a arewacin Somalia, a cewar Farfesa Clarke.

Manufar bincikenta shi ne bayar da haske ga ire iren wadannan wuraren wadanda ba a sani ba a duniya, kuma tana tsoron "za su bata babu wanda zai san su".