Shugaban da ya bayar da 'ya'yansa don yin gwajin rigakafin korona

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro, ya bayyana cewa 'ya'yansa biyu za su kasance cikin wadanda za a gwada rigakafin cutar korona da Rasha ta samar a kansu.
Masana kimiyya a fadin duniya na ci gaba da sukar rigakafin mai sunan Sputnik 5, saboda yadda Rasha ta samar da shi cikin hanzari ba tare da bayar da cikakken jawabi a kanta ba.
Da yake magana ta gidan talabijin din kasar, Mista Maduro, ya ce ya amince da shawarar da dan nasa ya yanke kuma da zarar an shirya fara allurar riga-kafi, su ne za su zamo na farko da za a fara yiwa.
A cewar alkalumman hukuma, an samu mutane dubu saba'in da bakwai da suka kamu da wannan cuta a Venezuela, adadin da 'yan adawa a kasar ke cewa ya zarta haka.
A yanzu haka, riga-kafin ta Rasha bata daga cikin jerin wadanda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta amince da su da suka kai matakai uku na gwaji, da ya hada da gwaje-gwaje sosai a kan dan adam.

Asalin hoton, Reuters
Da yake bayyana shi a matsayin na farko a duniya, shugaba Vladmir Putin na Rashan, ya ce riga-kafin, wadda cibiyar lafiya ta Gamaleya da ke Moscow ta samar, za ta kasance "garkuwa" game da cutar korona.
Ya kara da cewa yana sane cewa riga-kafin "zai yi aiki sosai ", ba tare da yin cikakken bayani kan abin da yake nufi ba, amma ya ce ta tsallake dukkan gwaje-gwajen da "ake bukatar yi a kansa".
Kazalika a karin bayanin da ya yi game da yadda 'yarsa ta yi amfani da riga-kafin, Mr Putin ya ce: "Bayan an yi mata allurar farko, yanayin zafin jikinta ya kai digiri 38, washegari ya yi kasa zuwa digiri 37.5, kuma shikenan. Bayan an yi mata allura karo na biyu, yanayin zafin jikinta ya yi sama kadan, sannan ya sake zama dai-dai."
Ba kasafai shugaba Putin yake magana kan 'ya'yansa mata - Maria Vorontsova da Katerina Tikhonova a bainar jama'a ba - kuma kusan dukkan rayuwarsu a cikin sirri take.











