Zaɓen Ghana na 2020: An nemi ƴan sandan Ghana su rage jima'i don shirya wa zaɓen ƙasar

Ƴan sandan Ghana

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar ƴan sandan Ghana ta bukaci jami'anta su rage yawan jima'i domin samn karfin da za su tunkari hayaniyar babban zaɓen kasar da za a gudanar a watan Disamba mai zuwa.

Kwamandan ƴan sandan yankin Accra na rundunar ƴan sandan, DCOP Afful Boakye-Yiadom ya ce kiran ya zama wajibi saboda yawan jima'i yana rage ƙarfi, kuma hakan zai yi tasiri a yunƙurin tabbatar da zaman lafiya lokacin zaɓe.

"Ku rage yawan jima'i, muna buƙatar ƙwazo a lokacin zaɓe, don haka ina ba ku shawara ku rika cin abinci sosai, ku rage yawan jima'i domin ku samu ƙarfin da za ku iya aiki a lokaci da kuma bayan zaɓen 2020", a cewar DCOP Afful Boakye-Yiadom.

Ya bayyana haka ne a lokacin da jami'an ƴan sandan suke gudanar da atisaye domin tabbatar wa ƴan ƙasar cewa a shirye rundunar take wajjen tunkarar zaben shugaban kasar na watan Disamba.

Babban jami'an ƴan sandan ya kuma shawarci jami'ansa su guji tsoma baki cikin harkokin siyasa domin kare kimarsu da ta aikin da suke yi.

Ana yawan tayar da jijiyoyin wuya a zaɓukan Ghana lamarin da kan sa jami'an tsaro yin damara sosai a duk lokacin da za a gudanar da zaɓe a kasar.

Ranar 7 ga watan Disamba ƴan kasar Ghana za su gudanar da zaben shugaban kasa, inda za a fafata tsakanin Shugaba Nana Akufo-Addo an jam'iyyar NPP da ke neman wa'adi na biyu, da kuma tsohon shugaban ƙasar John Mahama na jam'iyyar NDC wanda ke son sake ɗarewa kujerar mulkin ƙasar.