Sa baki a al’aura na jawo wa mata cuta a gabansu

Asalin hoton, Getty Images
Sa baki a al'aurar mata yau da kullum na jawo wa mata cuta a gabansu da ake kira BV, a wani bincike da mujallar kimiyar lafiya ta PLoS Biology ta wallafa.
BV ba cuta ba ce da ake yaɗawa ta hanyar jima'i. Kwayar cuta ce da yawanci ake samu ta hanyar sa baki a al'aurar mace.
Matan da suke ɗauke da cutar ba za su ji alamomi ba, amma kuma wasu za su dinga ganin ruwa mai wari na fita.
Masu bincike sun gano girman illar cutar da ake ɗauka a baki da yadda take rayuwa ta girma a al'aurar mace.

Game da BV
Kwayar cutar BV ba ta cika yin tsanani ba, amma ya kamata a gaggauta magance cutar da wuri domin samun cutar zai iya haifar wa mata cututtuka da ake samu wurin jima'i da kuma cutar mafitsara.
Idan mace tana da ciki, yana ƙara hatsarin haihuwar ɗan tayi.

Ta ya ake gane an kamu da cutar?
Ba sabon abu ba ne kuma matan da ke ɗauke da cutar za su dinga ganin wani ruwa da yake fita mai wari.
Za a ga sauyin yanayin fitar ruwan, zai koma fari-fari da ruwa-ruwa.
Likita zai iya buƙatar a yi gwaji domin tabbatar da ko ana ɗauke da kwayar cutar ta BV.
Idan har aka tabbatar da ana ɗauke da cutar, za a iya magance ta da magunguna ko mai na shafawa.

Me bincike ya gano?
Matan da ba sa ɗauke da cutar na dauke da wasu kwayoyi masu muhimmanci da ake kira lactobacilli da ke kare gaban mace.
A wasu lokuta wadannan sinadarai na iya raguwa da tasiri ko rage ruwan da ke ƙara wa mace ni'ima.
Babu cikakken bayanai kan abin da ke haddasa hakan, amma alamomin kamuwa da cutar sun haɗa da:
- Idan kina yawan yin jima'i (sai dai matan da ba su taba jima'i ba na iya kamuwa da BV)
- Sauyin abokin tarayya
- Amfani da IUD (allurar hana daukan ciki)
- Ko kina amfani da turare a kusa ko cikin al'aurarki
Binciken kimiyyar lafiya ta PloS Biology ya nuna yadda alakar cutuka da ake kamuwa a baki ko dadashi ke taimakawa wajen haddasa BV.
Sun yi gwaji a al'aura domin gano yadda wannan cuta take.
Cutar da ake dauka a baki, Fusobacterium nucleatu, na taimakawa wajen habaka sauran cutuka da ke janyo BV.
Masu binciken, Dr Amanda Lewis ta jami'ar California da abokan aikinta, sun ce sun gano yadda amfani da baki yayin jima'i ke taimakawa wajen haddasa cutar BV.
Masanan sun fahimci yadda BV ta samo asali daga jima'i, har a tsakanin mata 'yan maɗigo.
Farfesa Claudia Estcourt, kakakin kungiyar kwararru kan cutukan da ake dauka ta jima'i da HIV a Burtaniya, ta ce bincike irin wannan na da muhimmanci domin yana fahimtarwa kan cuta irin BV.
''Mun san cewa BV cuta ce mai sarƙaƙiya saboda akwai abubuwa da dama da ke janyo ta.''
Ta ce jima'i ta baki na yada cutuka da ake kamuwa da su ta jima'i da kwayoyin cuta da ke iya lahani ko rashin tasiri ga lafiya.












