Fyade: Mata na zanga-zanga kan matar da aka yi wa fyaɗe gaban ƴaƴanta a Pakistan

Mata sun fito zanga-zanga a manyan biranen Pakistan

Asalin hoton, FAROOQ NAEEM

Bayanan hoto, Mata sun fito zanga-zanga a manyan biranen Pakistan
Lokacin karatu: Minti 3

Hankalin ƴan Pakistan ya tashi bayan da wasu ƴan fashi suka yi wa wata mata fyaɗe a gaban ƴaƴanta a gefen babbar hanyar mota.

Amma ƙasar da cin zarafin mata ta hanyar lalata ya zama ruwan dare, ko me ya sa mutane suka fito game da wannan al'amarin a saman titi suna neman sauyi, tambayar da wakiliyar BBC Saira Asher ta yi kenan.

Mata a Pakistan ana ba su shawara a gida kada su fita da dare, ko kuma su tabbata sun fita tare da namiji a matsayin ɗan rakiya domin tsaronsu.

Amma wani babban jami'in ɗan sandan da aka ɗora wa alhakin gano maharan, ya fito ya dora laifin akan matar da aka ci zarafinta saboda fitowa da ta yi da dare ita kaɗai, lamarin da ya fusata ƴan ƙasar.

Kalamai da a baya ba a damu da su ba yanzu su ake kira ɗora laifi ga wanda aka ci zarafi.

"Dora laifi ga wanda aka ci zarafi, yanke hukunci ga wasu ɗabi'un mace don tantance ita aka ci zarafi; wannan ya samo asali cikin al'ummarmu tsawon shekaru," in ji Moneeza Ahmed, ɗaya daga cikin mata masu gwagwarmaya.

"Martanin alamu cewa yanzu al'ummarmu suna saurare, sun sauya kuma yanzu mata da dama suna magana."

Magoya bayan jam'iyyar ƴan uwa musulmi ta Jamaat-e-Islami lokacin da suke zanga-zanga kan adawa da matar da aka yi wa fyade a Lahore

Asalin hoton, ARIF ALI

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga na son a samar da sauyi kan kare hakkin mata.

Me ya faru a fyaɗen a kan titi?

Misalin ƙarfe uku na dare ranar 9 ga Satumba, fetur ɗin motar matar ya ƙare tana kan babbar hanyar gabashin birnin Lahore, kuma tana tare da ƴaƴanta biyu.

Ta kira ƴan uwanta a Gujranwala, waɗanda suka ba ta shawarar ta kira lambar ƴan kar ta kwana domin neman taimako.

A bayanan da ƴan sanda suka rubuta daga ɗaya daga cikin ƴan uwan matar, wasu maza biyu ƴan shekara 30 suka ɓalle motar suka saci kuɗi da zinarin da ke jikinta, suka yi mata fyaɗe a gaban ƴaƴanta biyu daga nan suka gudu.

Ƴan sanda sun ce har yanzu tana cikin damuwa, ko da yake ta ba su wasu bayanai game da siffofin waɗanda suka kai mata harin.

Bayan kwana ɗaya babban jami'in ƴan sanda a Lahore, Umar Shiekh ya fito gaban manema labarai yana ɗora laifin kan matar.

Ya ce me ya sa ba ta bi hanyar da mutane suke da yawa ba, tun da ta san ita kaɗai ce tare da ƴaƴanta, ko kuma ta duba yawan fetur ɗin da ke cikin motar kafin ta baro inda ta fito.

Ya nanata waɗannan kalaman a hirarrakinsa da kafafen yaɗa labaran talabijin, ya kuma ƙara da cewa matar da ke zama a Faransa ta ɗauka akwai zaman lafiya a Pakistan kamar Faransa.

Waɗannan kalamai sun fusata ƴan ƙasar musamman mata da suke mayar da martani a kafafen sadarwa na intanet

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

1px transparent line
Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

1px transparent line

Ministan kare haƙƙin ɗan Adam Shireen Mazari ya faɗi a Twitter: "Ga wani jami'i ya fito yana ɗora laifi ga matar da aka yi wa fyaɗe cewa kamata ya yi ta bi hanyar GT kuma me ya sa ta fita da dare da ƴaƴanta ba za a lamunce ba. Babu abin da zai goge laifin fyaɗe."

Hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta Pakistan ma ta yi allawadai da kalaman.

Mata na neman sauyi

Neman afuwa kan kalamansa ba abin da ya sauya kan fusata da mutane suka yi kan babban jami'in na ƴan sanda.

An gudanar da gangami a manyan biranen ƙasar. Daga cikin buƙatun sun hada da neman sauye-sauye ga tsarin aikin ƴan sanda, da kuma shari'a da tsarin gidan yari.

Supporters of the Civil Society hold a demonstration to condemn the incident of a woman gang raped on a deserted highway

Asalin hoton, Pacific Press

Ga waɗanda aka ci zarafi, wannan ba komai ba ne. A Paskitan kaɗan daga cikin shari'oin fyade ne aka zartarwa hukunci.

A wannan makon, gwamnati ta ce a majalisar dokokin ƙasar duk shekara a tsagaice ana samun laifukan da suka shafi fyaɗe 5,000 kuma kashi biyar ne ake yanke wa hukunci.

Ƙungiyoyi masu fafutika sun ce adadin ya fi haka, suna masu cewa yawancin laifukan fyaɗe ƴan sanda ake kai wa rahoto.

Mata na tsoron cin mutunci daga jami'an ƴan sanda da kuma tsangwama idan sun sanar da al'umma.

2px presentational grey line