Shugaban Zambia na makokin mutuwar wani kifi 'mai bayar da sa'a'

Asalin hoton, Edgar Lungu/Facebook
Shugaban Zambia Edgar Lungu ya bi sahun sauran 'yan kasar domin makokin mutuwar wani babban kifi da ake kiwonsa a ɗaya daga cikin manyan jami'o'i ƙasar, Jami'ar Copperbelt.
Kifin - da ake kira Mafishi - manyan yan siyasa da suka hada da mataimakan Shugaba Edar Lungu da shugaban ƴan adawa Hakainde Hichilema duk na jimamin mutuwarsa.
Kalmar Mafishi na ta jan hankali a shafin Tuwita a Zambia sakamakon mutuwar kifin tun cikin daren Litinin.
Daliban Jami'ar Copperbelt, CBU, sun kunna kyadura sannan suka yi jerin gwano inda suka kewaya jami'ar domin nuna alhinin mutuwar kifin.
Daliban jami'ar sun kwashe fiye da shekara 20 suna daukar kifin a matsayin abin da ke ba su sa'a a lokutan jarrabawa.
An yi amannar cewa Mafishi, abin da ke nufin "Babban Kifi" a harshen Bemba, ya shafe shekara akalla 22 kuma ya yi rayuwarsa ce a cikin gulbin da ke cikin jami'ar sama da shekara 20, a cewar shugaban dalibai Lawrence Kasonde said.
Ya kara da cewa ana gudanar da bincike kan mutuwarsa.
Mr Kasonde ya shaida wa BBC cewa: "Har yanzu ba a binne shi ba, muna tsara yadda za a kona shi."
Wasu daliban suka je wurin kifin kafin su rubuta jarrabawa inda suka yi amannar cewa yana ba su sa'a yayin da wasu ke kallonsa a matsayin wani abu da ke debe kewa, a cewar wakilin BBC a Zambia Kennedy Gondwe.
Shugaba Lungu ya ambato mai fafutukar kyamar mulkin mallaka na kasar India Mahatma Gandhi a sakonsa na jajen mutuwar kifin wanda ya wallafa a Facebook, yana mai cewa "ana auna girma da darajar kasa ne bisa yadda 'yan kasar suke mutunta dabbobin da ke cikinta".
"Ina farin ciki an yi makokinka yadda ya dace. Za mu yi kewarka," in ji shi.
Shugaban 'yan hamayya Hakainde Hichilema ya ce: "Muna jaje ga daliban CBU, wadanda suka wuce da wadanda suke nan, kan mutuwar shahararren kifi Mafishi."
A wani tsokaci da ya yi a shafin Twitter, @MoffatSamora ya ce: "Allah Ya jikansa. Mun aika da kwararrun lauyoyi da akawu su je su taimaka wa iyalansa kan wasiyyar da ya bari."












