’Yadda kifi ya yi tsalle ya bula min wuya’

Muhammad Idul sitting in hospital
Bayanan hoto, Sai Muhammad ya fada ruwa daga cikin kwale-kwalen.

Wani matashi a kasar Indonesia ya sha da kyar bayan wani katon kifi mai dogon baki ya kai masa hari a cikin ruwa.

Matashin ya yi bayani kan irin namijin kokarin da ya yi wajen linkaya domin tsira daga cikin teku bayan kifin ya kai masa hari.

Duk da cewa Muhammad Udul mai shekaru 16 yana raye kuma har ya samu damar bayar da labari dangane da abin da ya faru, ya yi godiya matuka ga likitocin da suka dage wajen yi masa tiyata domin ya warke.

Gargadi: Wannan labarin yana dauke da hotuna masu tayar da hankali.

Wannan ciwon da Muhammad ya samu sakamakon sukar da kifin ya yi masa ya sa ya yi suna a duniya inda aka yi ta yada hotunansa a shafukan intanet.

Amma a wata hira da ya yi da BBC kwanaki biyar bayan faruwar wannan mummunan lamari, ya ce lamarin ya faru ne yayin da suka je kamun kifi shi da wani abokinsa na makaranta mai suna Sardi inda suka fita da dare kuma aka samu bacin rana.

Ya bayyana cewa ''Kwale-kwalen da Sardi ya shiga shi ya fara tafiya, sai daga baya na shiga wani kwale-kwalen na bi shi''.

''Kusan tafiyar rabin kilomita daga gabar tekun, Sardi sai ya haska fitilarsa.''

''Sai wani kifi ya yi tsalle daga ruwa ya soke ni a wuya.''

Sai Muhammad ya fada ruwa daga cikin kwale-kwalen.

Dogon bakin kifin dai ya soke shi ne daga kasan gemunsa inda bakin kifin ya bi ta cikin wuyansa ya huda.

Abin mamaki shi ne kifin ya ci gaba da jan Muhammad cikin ruwa inda kifin ke neman ya gudu.

Hakan ya sa Muhammad ya rike kifin gam domin hana shi motsi sakamakon kada ya kara tsananta raunin da ya ji masa.

''Na roki Sardi da ya taimaka mani - ya hana ni kokarin cire kifin domin ka da na zubda jini da yawa,''in ji Muhammad.

Muhammad ya yi kokari ya yi linkaya zuwa bakin teku rike da kifin mai tsawon santimita 75 a hannunsa kuma bakin kifin makale a cikin wuyansa.

Mahaifin Muhammad ya garzaya da shi asibiti a garin Bau-Bau, kusan sa'a daya da rabi kenan daga kauyensu.

Duk da likitocin sun yi kokarin yanke kifin, kan kifin kawai ya rage a jikin Muhammad sakamakon rashin kayan aikin da za su yi amfani da su domin cire tsinin bakin kifin daga wuyansa.

A wannan dalili ne ya sa dole suka kara tafiya zuwa wani asibiti da ke lardin Makassar.

Duk da cewa asibitin da suka je a wannan karon babba ne, ma'aikatan asibitin sun ji tsoro da suka ga abin da ya faru da Muhammad.

Daraktan asibitin Khalid Saleh ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da suke samun irin wannan lamarin, don haka suna bukatar kwararrun likitoci biyar domin su bi a hankali wajen cire abin da ya rage na daga kifin a jikin Muhammad.

An dai shafe sa'a daya da rabi kwararrun likitocin suna tiyata kafin su gama tiyatar cire tsinin bakin kifin.

Bayan kwanaki biyar, Muhammad ya kosa ya koma gida, an daure wuyansa da bandeji, kuma ciwon baya yi masa zafi ko kadan.

Amma duk da haka, ba ya iya juya wuyansa zuwa hannun dama, amma dai Muhammad yana murmushi.

Wannan dalili ne ya sa dole zai kara zama a asibiti ya kara warwarewa kafin ya koma gida.

Daraktan asibitin ya shaida wa BBC cewa, ''muna lura da lafiyarsa, za mu iya sallamarsa nan da kwanaki kadan, amma ba zai iya komawa kauye ba domin yana bukatar a kara yi masa wasu gwaje-gwaje.

Amma duk da wannan abin da ya faru, Muhammad bai daina kaunar kifi ba.

Ya , ''Nan gaba zan rika taka tsan-tsan. Irin wannan kifin ba ya son haske, shi ya sa ya yi tsalle ya fito daga ruwa ya soke ni''.Wani matashi a kasar Indonesia ya sha da kyar bayan wani katon kifi mai dogon baki ya kai masa hari a cikin ruwa.

Needlefish in boy's neck

Asalin hoton, Facebook