Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Bayanin ban mamaki kan yadda cutar korona ba ta kashe mutane sosai ba a Afrika
- Marubuci, Daga Andrew Harding
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC Afrika a Johannesburg
Akwai alaƙa tsakanin talauci, cunkoson wurin kwana da kuma mamakin da ake yi kan yadda cutar korona ba ta kama 'yan Afirka ko haddasa mace-mace sosai ba?
Yayin da alkaluman masu kamuwa da cutar ke jan baya a Afirka Ta Kudu, da kuma koma-bayan da take a nahiyar, masana sun kai wani mataki na nazari.
Yankuna masu cunkoso da rashin tsafta da rashin yiwuwar bai wa juna tazara tsakanin al'umomin yankunan da aka tara iyalai na rayuwa a ɗaki daya tal.
A tsawon watanni, ƙwararru a fannin lafiya sun sha gargadi cewa rayuwar talaucin da ake ciki, a yankunan birane a sassan Afirka na iya ba da gudunmawa wajen sake ta'azzara bazuwar cutar korona.
''Yawan al'umma na daga cikin muhimman abin da ake magana a kai. Idan ba ku da damar bai wa juna tazara,'' a cewar Farfesa Salim Abdool Karim, shugaban kwamitin da ke bada shawarwari kan Covid-19 a Afrirka Ta Kudu.
To yaya kenan idan abin da ake tunani ya kasance ba haka ba?
To yaya kenan idan ya kasance wadannan wurare masu cunkoso su ne amsar mamakin da masana ke yi kan nahiyar a tsawon watanni?
To ko yana iya kasancewa - mu sa shi ta wannan hanyar - talauci shi ne jigo ko babbar kariya ga Covid-19?
'Akwai sarƙaƙiya'
Bari mu soma kan wanda ya fi ban mamaki.
A kwanakin farko na bullar annobar, ƙwararru baki daya da masana sun yi amannar cewa Afrika na cikin tsaka mai wuya.
''Na yi tsammanin muna gab da faɗawa cikin bala'i, wanda babu mafita,'' a cewar Farfesa Shabir Madhi, babban masanin kan ƙwayoyin cutuka a Afirka Ta Kudu.
Duk da cewa wani hasashen da aka yi na'am da shi na cewa asibitocin kasa - a kasashen da aka fi samun ci gaba a nahiyar - za su kure ko fin ƙarfin asibitocinsu a cikin gaggawa.
Kuma har yanzu, Afirka Ta Kudu na farfadowa daga bugun farko da annobar korona ta yi mata, ko da dai adadin mamatan ba su kama ƙafar Burtaniya ba.
Ko da a ce alkaluman mamatan akwai kuskure a ciki - watakil saboda wasu dalilai - Afirka Ta Kudu ta ba da mamaki sosai, haka zalika wasu ƙasashen yankunan, da gadajen asibitoci babu kowa a kai, da kuma inda aka daina ko samun ragin alkaluman masu kamuwa da cutar, yayin da wasu ƙasashen duniya ke ta fama.
''Yawancin ƙasahen Afirka ba su kai ƙololuwa ba. Ban san dalili ba. Na nutse a kogin tunani,'' a cewar Farfesa Karim, muryar da ke yaƙar korona a Afirka Ta kudu.
Farfesa Madhi ya amince: ''Akwai sarƙaƙiya. Abin akwai wuyar amincewa.''
A ƴan kwanakin nan, ƙwararru sun ba da misali da yawan matasa a matsayin bayanin da ake alaƙantawa da ƙarancin kamuwa da cutar.
Ko da yake adadin matasan bai zarce rabin wanda ake da shi a Turai ba.
Ƴan Afirka ƙalilan ake iya alaƙanta wa da shekarun 1980, sannan wannan na iya zama dalili da ya yi tasiri wajen yaƙar annobar.
''Yawan shekaru na daga cikin misalai na barazanar cutar. Ƴan Afirka masu ƙanƙantar shekaru sun nuna adawarsu da haka,'' a cewar Tim Bromfield, darakta a cibiyar Tony Blair.
Amma yayin da annobar ke cigaba, sannan ake samun sahihan bayanai, masu sharhi na sake nuna rashin damuwa domin bada cikakkun bayanai kan nasarorin nahiyar.
''Shekaru ba wai kawai shi ne wani jigo mai karfi ba,'' in ji Farfesa Karim.
Da fari, dokar kulle da ya fusata mutane a Afirka ta kudu da sauran ƙasashen Afirka ya taka muhimmiyar rawa.
Bukatar amfani da takunkumi da samar da iskar da ke taimakawa numfashi sun taimaka.
Wasu labaran masu alaƙa:
Sauran bayanai - kan tasirin yanayi ko zafi - an tura su gefe guda.
Wasu ƙwararru sun gargadi cewa ƙasashe masu fama da talauci watakil sun samu aron lokaci ne, sannan mai yiwuwa annobar ta dawo da karfinta a ɓarkewar karo na biyu cikin ƴan watanni.
''Ba zan yi saurin yanke hukuncin cewa Afirka ta wuce shiga yanayi mafi muni. Kuma ba ni da tabbacin ko wata rana annobar za ta yadu babu sassauci,'' in ji Farfesa Karim.
Cutar korona da tsarabarta
A ƴan kwanakin da suka gabata, masana kimiya a sashen riga-kafi da cututtuka masu yaduwa, a asibitin Baragwanath a Soweto, na mamakin abin da aka gaggara ganowa -amsa da suke son sani kan yadda nahiyar ta ci ƙarfin korona.
Maganar ita ce, idan kana karantun PDMCs, masanan na iya samun hujjar cewa mutane da dama sun kamu da korona - misali, yadda galibin mutane suka rinƙa mura - saboda watakil sun kamu da cutar amma garkuwarsu tana da ƙarfi.
''Akwai rabe-rabe a ciki. Wasu dalilai da a baya ake yawaita samu a yankunan... na iya gamsar da bayanai kan dalilan da suka sa annobar ba ta yadu ba (kamar yadda aka gani a wasu sassa ko yankunan duniya),'' a cewar Farfesa Madhi.
Mura da massasara, babu shaka cututtuka ne da ake yi kusan a ko ina a duniya.
Sai dai masanan daga Afirka Ta Kudu na nuna shaku, saboda irin wadannan cututtuka sun fi saurin yaduwa a inda ake da mutane da yawa, matalauta ake yi wa kallon za su fi shiga barazana.
Kuma kusan abin da ya faru kenan a wasu sassan duniya, kamar Indiya, da ke da makamancin wannan ƙalubale.
Sai dai yayin da masana suka duƙufa shirye-shiryen gwajin PBMC a daƙin gwaje-gwaje, sun gamu da matsala.
''Mun yi mamaki matuƙa. Duk a shirye muke amma haƙiƙa wannan abu ya faru,'' in ji Dakta Guarav Kwatra, da ke jagorantar gwajin.
Babu wanda za a dorawa alhaki - kawai dai yanayi ne wanda a ko da yaushe ana iya tsintar kai a ciki.
Yanzu haka tawagar na farautar sake sabbin gwaje-gwaje, amma yana iya daukar tsawon watanni.
Amma a yanzu dai babu shaka Afrika ta ba da mamaki duk da cewa akwai annobar.