Hotunan auren mutum 6,000 duk da fargarbar corona a Koriya ta Kudu

Dubban ma'aurata ne suka halarci gagarumin bikin da gidauniyar nan mai taimakon al'umma da assasa zaman lafiya ta Family Federation for World Peace and Unification ta shirya, wanda aka yi a Cocin Unification da Gapyeong a Koriya ta Kudu.

An gudanar da bikin ne a cibiyar Heongshim Peace World Centre a Gapyeongin, da ke kusa da babban birnin kasar Seoul.

An yi bikin ne duk da fargabar da ake da ita ta yaduwar cutar coronavirus wadda ta samo asali a Wuhan na kasar China.

Tuni dai kasar ta Koriya Ta Kudu ta tabbatar da cewa an samu mutum 24 da suka kamu da cutar a kasar.

Wasu daga cikin ma'auratan sun sanya abin rufe fuska a wajen bikin, to amma kuma ba kowa ne yake ganin sanya abin rufe fuskar zai iya yin kariya ba.

Kusan mutum 6,000 da suka fito daga kasashe fiye da 60 ne aka aurar a wajen bikin. Bikin da gidauniyar ta jima ba ta yi irinsa tun a shekarar 1960.

An dai dudduba dukkan wadanda suka halarci bikin kafin su shiga ciki domin gudun ko akwai mai alamar cutar a tare da shi.

An soke duk wasu manyan taruka da aka shirya yi a Koriya Ta Kudu, kuma cocin da ya shirya bikin ya haramtawa duk wasu ma'aurata daga China halartar gagarumin bikin.

Cocin dai wato inda aka yi bikin a ciki ya raba wa mutum dubu 30 abin rufe fuska, amma kuma ba kowa ba ne ya sanya nasa.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka