Hotunan auren mutum 6,000 duk da fargarbar corona a Koriya ta Kudu

Dubban ma'aurata sun halarci bikin da aka yi a Unification church da ke Seoul

Asalin hoton, Reuters

Presentational white space

Dubban ma'aurata ne suka halarci gagarumin bikin da gidauniyar nan mai taimakon al'umma da assasa zaman lafiya ta Family Federation for World Peace and Unification ta shirya, wanda aka yi a Cocin Unification da Gapyeong a Koriya ta Kudu.

An gudanar da bikin ne a cibiyar Heongshim Peace World Centre a Gapyeongin, da ke kusa da babban birnin kasar Seoul.

An yi bikin ne duk da fargabar da ake da ita ta yaduwar cutar coronavirus wadda ta samo asali a Wuhan na kasar China.

Tuni dai kasar ta Koriya Ta Kudu ta tabbatar da cewa an samu mutum 24 da suka kamu da cutar a kasar.

Wata amarya sanye da abin rufe fuska domin kariya daga cutar coronavirus, ta halarci bikin d aaka aurar da mutum 6000

Asalin hoton, Reuters

Presentational white space

Wasu daga cikin ma'auratan sun sanya abin rufe fuska a wajen bikin, to amma kuma ba kowa ne yake ganin sanya abin rufe fuskar zai iya yin kariya ba.

Wata amarya ta dauki hoton selfie a wajen wani gagarumin biki da cocin Unification a Seoul ya shirya.

Asalin hoton, AFP

Presentational white space

Kusan mutum 6,000 da suka fito daga kasashe fiye da 60 ne aka aurar a wajen bikin. Bikin da gidauniyar ta jima ba ta yi irinsa tun a shekarar 1960.

Ana duba mahalarta bikin ta hanyar amfani da abin gwada zafin jikin mutum a wajen bikin da aka aurar da mutum 6000

Asalin hoton, Getty Images

Presentational white space

An dai dudduba dukkan wadanda suka halarci bikin kafin su shiga ciki domin gudun ko akwai mai alamar cutar a tare da shi.

An soke duk wasu manyan taruka da aka shirya yi a Koriya Ta Kudu, kuma cocin da ya shirya bikin ya haramtawa duk wasu ma'aurata daga China halartar gagarumin bikin.

Ma'aurata na shirye-shiryen irin rawar da za suyi a wajen gagarumin bikin da cocin Unification ya shirya a Koriya ta Kudu.

Asalin hoton, AFP

Presentational white space
Ma'aurata na shirye-shiryen irin rawar da za suyi a wajen gagarumin bikin da cocin Unification ya shirya a Koriya ta Kudu.

Asalin hoton, AFP

Presentational white space
Ma'aurata a wajen gagarumin bikin da cocin Unification ya shirya a Gapyeong.

Asalin hoton, Getty Images

Presentational white space

Cocin dai wato inda aka yi bikin a ciki ya raba wa mutum dubu 30 abin rufe fuska, amma kuma ba kowa ba ne ya sanya nasa.

Wata amarya ta na duba wayar salularta a wajen gagarumin bikin da cocin Unification ya shirya a Gapyeong.

Asalin hoton, Woohae Cho

Presentational white space
Ma'auratan na tattaunawa a yayin bikin da aka yi

Asalin hoton, AFP

Presentational white space
Wasu ma'aurata sun sanya abin rufe fuska inda suka halarci gagarumin bikin da cocin Unification ya shirya a Gapyeong.

Asalin hoton, AFP

Presentational white space
Ma'aurata na sanya wa juna zobe a wajen gagarumin bikin da cocin Unification ya shirya a Gapyeong

Asalin hoton, AFP

Presentational white space
Ma'aurata na murna da shewa a wajen gagarumin bikin da cocin Unification ya shirya a Gapyeong

Asalin hoton, AFP

Presentational white space

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka