Coronavirus: Shin bazuwar cutar korona na raguwa a Afirka?

    • Marubuci, Daga Peter Mwai and Christopher Giles
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ƙarfin yaɗuwar annobar cutar korona a Afirka ya wuce, amma ta yi gargaɗi ga gwamnatoci kada su saki jiki yayin da ƙasashe suka sassauta dokar kulle.

Yawan waɗanda ke kamuwa da cutar a kullum na raguwa a tsawon wata ɗaya, ko da yake wasu ƙasashen adadin ƙaruwa yake.

Me muka sani game da dalilin cutar a Afirka?

A wane mizani cutar korona ke bazuwa?

A tsawon makwanni huɗu da suka gabata, an samu raguwar yaɗuwar cutar da kashi 17 daga yawan alƙaluman da ake bayar da rahotanni a mako.

"Abin da muka sani ya kasance mafi girma, amma kuma yanzu yawan masu kamuwa a rana da ake bayar da rahoto na raguwa a yankunan," in ji shugabar WHO a yankin Afirka Matshidiso Moeti.

Zai iya kasancewa saboda adadin da ke ƙaruwa ya ragu a wasu ƙasashe masu yawan jama'a a yankin kamar Afirka ta kudu da Masar da Najeriya.

Amma ana samun ƙaruwar cutar a wasu ƙasashe kamar gabashi da arewacin Afirka, a cewar hukumar ɗakile cutuka masu yaɗuwa a Afirka (CDC).

A Uganda da Rwanda an samu ƙaruwar cutar a kwanakin baya, yayin da adadin ya ragu a ƙasashen Kenya da Somalia.

A ƙasashen arewacin Afirka Morocco da Tunisia ma adadin ya ƙaru, haka kuma an samu ƙaruwar wadanda suka kamu a Libya, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.

Amma, a Aljeriya da Masar adadin ya ragu a watannin da suka gabata. Sauran ƙasashen da aka samu raguwar masu kamuwa da cutar sun haɗa da Ghana da Gabon da Madagascar da Zambia.

Hukumar ayyukan jin kai ta duniya International Rescue Committee, ta ce ba a fito da gaskiyar girman annobar ba saboda ƙarancin gwaji da kuma matsalar da ta shafi samun bayanai.

Kuma Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce dole a yi taka tsantsan da alƙalumanta domin za su iya sauyawa saboda gwaji da kuma rashin samun bayanai.

Wasu ƙasashen sun yi watsi da yin gwaji a wasu wurare sai dai a wuraren da aka samu masu ɗauke da cutar.

Wasu kuma kamar Habasha sun ƙarfafa gwaji ta hanyar faɗakarwa tare da fatan yi wa mutane 400,00 gwaji a wata ɗaya. Yanzu kuma an samu ƙaruwar yawan masu cutar.

Ina ne cutar ta fi ƙamari a Afirka?

Hukumar CDC ta Afirka ta ce yawan masu cutar a ƙasashe biyar kawai sun kai kashi 72.

Afirka ta Kudu ce ke da yawan masu ɗauke da cutar da kuma yawan waɗanda cutar ta kashe a Afirka, kuma ta biyar a duniya da cutar ta fi yaɗuwa.

Yawan waɗanda ke mutuwa ba su kai na sauran ƙasashen duniya da cutar ta fi yi wa illa ba.

Yawan waɗanda ake kwantarwa a asibiti a kullum na raguwa, amma yawan masu mutuwa ba su raguwa.

Amma sauyin tsarin gwaji a Afirka ta Kudu yana da tasiri ga yawan waɗanda ake bayar da rahoto.

"Tsarin gwajin ƙasar a yanzu shi ne gwajin waɗanda kawai suka nuna alamomin cutar yana bayar da wahalar tantance yawan masu cutar," Inji WHO.

Wani binciken cibiyar binciken lafiya ta Afirka ta Kudu (SAMRC) ya nuna cewa yawan mutanen da suka mutu sakamakon kwayar cutar zai iya zarce adadin waɗanda aka ruwaito.

Binciken ya nuna cewa ƙaruwar masu mutuwar wanda ya bambanta da mace-macen a wani lokaci ya ƙaru da 17,000 - wato ƙari da kashi 59 idan aka kwatanta da shekarun baya.

Lardin Gauteng wanda ya ƙunshi Johannesburg, shi ke da fiye da kashi uku na yawan masu ɗauke da cutar. Amma lardin yammacin Cape (Inda Cape Town ta ke) an fi mutuwa.

Masar ita ce ta biyu da yawan wadanda suka mutu, amma an samu raguwar masu kamuwa da cutar.

Mutum nawa ke mutuwa a Afirka?

Yawan masu mutuwa yanzu ya ragu idan aka kwatanta da sauran sassan duniya duk da matsalolin kiwon lafiya a yawancin ƙasashen Afirka.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce wannan saboda yawan al'ummar Afirka matasa ne - sama da kashi 60 ƴan kasa da shekara 25 ne. Cutar korona ta fi kama masu manyan shekaru.

Matsalolin lafiya da yawanci aka fi samu a manyan ƙasashe kamar ƙiba da ciwon suga, ba a cika samu ba a Afirka.

Idan aka yi la'akari da yawan waɗanda suka kamu da korona suka mutu, akwai ƙasashe tara na Afirka

Sai dai idan ba a fiye gwaji ba, ba za a samu yawan masu cutar ba, kuma yawan masu mutuwa za su ƙaru.

Ya girman gwaji a Afirka?

Yawan gwajin da aka yi a ƙasashe 11 ya kai kashi 80 - Afirka ta Kudu da Morocco da Habasha da Masar da Ghana da Najeriya da Rwanda da Mauritius, da kuma Kamaru.

Akwai bambanci a yawan gwajin, inda aka fi yi a Afirka ta Kudu amma ba a yi a Najeriya duk da yawan jama'arta, kamar yadda alƙaluman cibiyar da ke tattara bayanai kan cutar korona ta Our World in Data, suka nuna

Daga 18 ga Agusta Afirka ta Kudu ta yi gwaji 58 kan mutum 1,000, idan aka kwatanta da 180 a Birtaniya da kuma 208 a Amurka.

Najeriya kuma kashi 1.7 kan mutum 1,000, yayin da Kenya ta yi kashi 7.4 Ghana kuma kashi 13.9.

Kasashen da suka aiwatar da gwaji sama da 100 sun haɗa da Uganda da Rwanda da Mauritius.

Yana da kyau a nuna cewa wasu ƙasashen Afrika yana da wahala a iya gane abin da ke faruwa saboda rashin bayanai.