Zaben Nijar 2020: Rikici ya kunno kai kan katin zabe a jamhuriyar Nijar

Rikici ya kunno kai a Jamhuriyar Nijar kan katin masu zabe bayan hukumar zaben kasar ta bayyana cewa katin bana zamani bane sabanin yadda tayi alkawari.
Tuni dai 'yan siyasa da masu fafutuka suka yi alawadai da wannan mataki suna masu cewa wata hanya ce ta yin magudi a zaben kasar mai zuwa.
'Yan siyasar kasar sun ce katin zabensu da suka saba amfani da shi ya fi wannan da za a samar a yanzu.
A wajen wani taron siyasa ne hukumar zaben ta bayyana cewa katin zaben bana zamani bane abin da bai yi wa 'yan siyasar dadi ba musamman wadanda suka fito daga jam'iyyun hamayyar kasar.
Jam'iyyar MDND Kokari ta bakin shugabanta ta ce, dubun hukumar zaben ne ya cika.
Shugaban jam'iyyar ta MDND Kokari Annabo Samaila, ya shaidawa BBC cewa "Yau gaskiya ta bayyana, mu dama mun san babu zabe saboda bamu shirya komai ba, kuma katin zabe na biometric wato a zamani shi ne yakamata a samar ta yadda za a bawa kowa yaje ya kada kuri'arsa a ranar zabe".
Ya ce wannan kati na damfara ne, kuma da shi ne ake so ayi zabe dashi domin da wannan kati da suka samar a yanzu, mutum 100 za su iya yin zabe da guda inji shugaban jam'iyyar ta MDND Kokari.

Asalin hoton, Getty Images
Sauran jam'iyyun siyasar kasar 'yan ba ruwanmu kuwa cewa suka yi dama sun san wannan rana zata zo domin basu da gaskiya.
To sai dai kuma a bangaren jam'iyyu masu mulki a kasar sun ce yakamata hukumar zaben kasar ta sake tunani a kan wannan kati data fito dashi.
Dakta Sita, shi ne shugaban gungun jam'iyyu masu mulkin kasar ya shaida wa BBC cewa,"SENI, ta kara zurfin tunani, don katin nan na zabe ba a son mutum guda da wannan kati ya y zabe biyu zuwa uku".
A nasu bangaren masu fafutukar kare hakkin farar hula a kasar sun ce basu yar da asa kasarsu a cikin wani mugun yanayi ba,
Tuni dai hukumar zaben kasar SENI, ta sha alwashin samar da mafita ga wannan matsala.
Wannan dai na faruwa ne a yayin da ya ya rage watanni hudu a soma zaben kasar ta Nijar.











