Muhimman abubuwan da za su faru a shekarar 2020

A

Asalin hoton, INTI OCON

    • Marubuci, Daga Nabeela Mukhtar Uba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist

Yayin da aka yi bankwana da shekarar 2019, BBC ta yi nazari kan wasu muhimman abubuwan da za su faru a cikin shekarar 2020.

Daga cikin abubuwan akwai:

1. Kaddamar da kudin bai daya na kasashen yammacin Afirka

A

Asalin hoton, AFP Contributor

Kasashen da suka amince su fara amfani da sabon kudin a 2020 sun hada da Benin da Burkina Faso da Guinea-Bissau da Code d'Ivoire da Senegal da Togo da Mali da kuma Nijar.

Ghana ma ta bayyana kudirinta na shiga wannan tsari.

Yawanci kasashen sun yi amannar cewar rungumar tsarin na amfani da kudin bai-daya zai taimaka wajen saukaka harkokin cinikayya da samar da tsayayyen tsarin kasuwanci a tsakaninsu.

2. Najeriya za ta cika shekara 60 da samun 'yancin kai

A

Asalin hoton, KOLA SULAIMON

Bayanan hoto, Najeriya ta samu 'yancin kai ne a ranar 1 ga watan Oktoban 1960

Ranar 1 ga watan Oktobar 2020 Najeriya ke cika shekara 60 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallakar Burtaniya.

A shekarun baya, an sha soke bikin murnar samun 'yancin kai a Najeriyar tare da shirya kwarya-kwaryan taro don murnar ranar saboda matsalolin tsaro. Yayin bikin, shugaban kasa na yi wa 'yan kasar jawabi kan nasarorin da kasar ta samu da kuma irin abubuwan ci gaban da gwamnati za ta samar.

3. Zaben shugaban kasa ajamhuriyar Nijar

A

Asalin hoton, ISSOUF SANOGO

A watan Disamba za a gudanar da zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar.

Za a gudanar da zaben ne bayan Shugaba mai ci, Mouhammadou Issofou ya kammala wa'adin mulkinsa.

A yanzu, jam'iyya mai mulki a kasar, PNDS Tarayya ta tsayar da Bazoum Muhammad a matsayin wanda zai yi ma ta takara.

4. Zaben shugaban kasa a Ghana

A

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Shugaba mai ci Nana Akufo-Addo ya sanar cewa zai sake tsayawa takara a watan Disambar 2019

Za a gudanar da zaben shugaban kasar Ghana a karshen shekarar 2020.

A watan Fabrairun 2019, jam'iyyar hamayya ta NDC ta sanar da tsohon shugaban kasar John Mahama a matsayin wanda zai yi mata takara.

A watan Disambar 2019 kuma shugaba mai ci Nana Akufo-Addo ya sanar cewa zai sake tsayawa takara.

Mutanen biyu dai sun taba fafatawa a 2012 inda Mahama ya yi nasara sannan kuma a 2016, Akufo-Addo ya lashe zabe.

5. Zaben shugaban kasa a Amurka

A

Asalin hoton, Scott Olson

Bayanan hoto, Zaben na Amurka zai ja hankali musamman yadda ake ganin batun tsige Shugaba Trump zai yi tasiri a zaben

Za a gudanar da zaben shugaban kasa a Amurka ranar Talata 3 ga watan Nuwambar 2020.

Zaben na Amurka zai ja hankali musamman yadda ake ganin batun tsige Shugaba Donald Trump zai yi tasiri a zaben. Majalisar wakilan Amurka ta tsige Trump bayan da ta same shi da laifin yi wa majalisar karen tsaye da wuce hurumin ofishinsa.

Wasu daga cikin manyan 'yan takarar da za su fafata a zaben karkashin jam'iyyar Republican akwai Trump da Joe Walsh yayin da Joe Biden da Michael Bloomberg da Bernie Sanders za su tsaya takara karkashin inuwar jam'iyyar Democrat.

6. Zaben 'yan majalisar dokoki a Masar

A

Asalin hoton, ODD ANDERSEN

Bayanan hoto, A baya an tsara gudanar da zaben a watan Afrilu ko Mayun 2020

An tsara gudanar da zaben a watan Nuwambar 2020 domin tsayar da wakilai da sanatoci.

A baya an tsara gudanar da zaben a watan Afrilu ko Mayun 2020.

Sai dai Shugaba Abdel Fattah el Sisis ya umarci majalisar dokokin kasar ta dakatar da ayyukanta a ranar 1 ga watan Oktobar 2019 tare da bai wa hukumar kula da tsaron kasar ragamar fitar da jadawalin 'yan takara.

Ya yi haka ne saboda rashin gamsuwa da tsarin da ofishin da ke kula da bayanan sirri ya bi wajen zabar 'yan takara a zaben 'yan majalisar da ya gabata.

7. Bikin kama kifi na Argungu

A

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

Bayanan hoto, An fara bikin ne a shekarar 1934

Ana gudanar da bikin duk bayan shekara hudu a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.

An fara bikin a shekarar 1934. Ana gudanar da bikin a matsayin wata alama ta kawo karshen rashin jituwa tsakanin masarautar Kebbi da Daular Usmaniyya.

An dakatar da bikin a baya sakamakon matsalolin tsaro da aka yi ta fama da su.

8. Janye sojoji daga wasu sassan Najeriya

A

Asalin hoton, AUDU MARTE

Bayanan hoto, Gwamnatin Najeriya za ta dauki matakin janye sojojin domin bai wa 'yan sanda da sauran jami'an tsaron da ba sojoji ba damar tsare yankuna

Gwamnatin Najeriya za ta dauki matakin janye sojojin ne domin bai wa 'yan sanda da sauran jami'an tsaron da ba sojoji ba damar tsare wasu yankunan kasar.

Mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya ce "matakin wata manuniya ce kan yadda ake samun ci gaba a fannin tsaro a wasu sassan kasar."

Sai dai bai bayyana yankunan da janye sojojin zai shafa ba tukuna, amma ya ce hakan ba zai shafi yankin arewa maso gabashin kasar ba.

9. Ficewar Burtaniya daga Tarayyar Turai

Boris Johnson outside Downing Street

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jam'iyyar Conservatives ta Firai Minista Boris Johnson ce take da rinjaye a majalisar Burtaniya da kujeru 80

A ranar Juma'a 31 ga watan Janairu ne ake sa ran Burtaniya za ta fice daga Tarayyar Turai bayan 'yan Majalisar Dokokin kasar sun amince da daftarin Firai Minista Boris Johnson na ficewar kasar.

10. Gasar cin kofin nahiyar Turai EURO 2020

eURO 2020

Asalin hoton, Getty Images

Za a gudanar da gasar a birane 12 a kasashen Turai daga 12 ga watan Yuni zuwa 12 ga watan Yulin 2020.

Portugal ce mai rike da kambun gasar bayan da kasar ta lashe gasar a shekarar 2016.

Za kuma a yi amfani da na'urar VAR a karon farko a gasar.

11. Gasar motsa jiki ta Olympics da za a gudanar a Tokyo

A

Asalin hoton, BEHROUZ MEHRI

Bayanan hoto, Wannan shi ne karo na uku da za a gudanar da irin gasar a yankin gabashin Asia

Gasar ta Olympics za ta soma daga 24 ga watan Yuli zuwa 9 ga watan Agustan 2020 a Tokyo da ke Japan.

Kwamitin tsara gasar Olympics ne ya zabi Tokyo a matsayin mai masaukin baki a wani taronsa karo na 125 da aka gudanar a Buenos Aires da ke Argentina.

Wannan shi ne karo na uku da za a gudanar da irin gasar a yankin gabashin Asiya.