Zaben Nijar 2020: Yadda tsarin zaben shugaban kasa yake

Zabe a nijar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Domin bai wa 'yan kasar da suka kai zabe damar gudanar da 'yancinsu na 'yan kasa ne hukumar zaben kasar CENI ta shirya rangadi a fadin kasar domin yi wa mabukata takardun haihuwa

A jamhuriyyar Nijar, yanzu haka shirye-shiryen zabubuka masu zuwa sun kankama. Baya ga na hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta CENI, jam'iyyu da 'yan takara na ci gaba da shirya taruruka dan ganawa da magoya bayansu.

Kawo yanzu dai 'yan takara daga jam'iyyun siyasa daban-daban 12 ne suka bayyana kansu don neman kujerar shugabancin kasar a zabubukan da za su gudana a 2020-2021. Abin tambaya a nan shi ne shin ko yaya tsarin zaben shugaba kasar yake?

Tchima Illa Issoufou wadda wakiliyar BBC ce a birnin Yamai ta amsa mana wannan tambaya:

Kuri'un da ake bukata ga shugaban kasa

A zagayen farko na zaben shugaban kasa 'yan takarar na fita ne da zummar neman kashi 50.1 na kuri'un da za'a kada abun da zai ba su damar zarcewa a zagayen farko ba tare da an je zagaye na biyu ba.

To sai sai dai in hakan ta kasa samuwa ne hukumar zaben ke daukar wanda ya zo na daya da na biyu a yawan kuri'u don su fafata a zagaye na biyu.

Hakan ne ma ya sa hukumar zaben kasar ta bayyana ranar 21 ga watan Fabrairun 2021 a matsayin ranar da za'a gudanar da zaben zagayen na biyu na shugaban kasa.

'Yan takara da jam'iyyu da suka kasa kai bantansu na shiga jam'iyyar da ta zo ta biyu a yawan kuri'un da aka jefa domin kulla kawancen da zai ba su damar cin zaben.

Ana kulla kawancen bisa wasu yarjeniyoyi da ba su saba wa tsarin mulkin kasar ba. Kundin tsarin mulkin kasar ta Nijar ya haramta wa jam'iyyu yin kawance kan rabon mukamai abun da tsarin mulki ya ce ya zama cin hanci.

Mace na kada kuri'ara a zaben Nijar
Getty
Wasu bayanai kan zaben Nijar na 2020

  • 147Yawan jam'iyyun siyasa a Nijar

  • 20Yawan 'yan takarar shugaban kasa a zaben 2020

  • Miliyan 21Yawan al'ummar kasar

  • Miliyan 9Yawan mutanen da suka yi rijistar zabe

Bayanai: Hukumar Zabe Ta Nijar

Ja-in-ja kan rijistar masu zabe

Sai dai duk da nanata aniyarsu ta shiga zabubukan masu zuwa jam'iyyu masu adawa na ci gaba da kaurace wa duk wasu ayyuka da hukumar zaben kasar ke yi baya ga rijista da suka umurci magoya bayansu su fito su yi, sai kuma kasancewar wakilansu cikin kananan komitocin kula da rijistar ta masu zabe.

Jam'iyyun siyasar na bangaren adawa na zargin hukumar zaben da zama 'yar amshin shatar gwamnati abun da ya sa ma suka bukaci shugaban kasa ya rushe hukumar zaben dan maye gurbinta da wata sabuwa da za ta kunshi kowa da kowa.

Ko da a ranar Alhamis yayin da hukumar zaben ke ganawa da 'yan siyasa, kawancen jam'iyyun adawa ya kira wani taro na daban, inda ya kaddamar da wani littafi da suka yi wa suna Livre Blanc ko farin littafi da ke zancen kalubale da matsalolin da suka dabaibaye shirye-shiryen zabubukan masu zuwa.

Litaffi ya zayyana daya bayan daya tare da bayar da cikakkiyar shaidar rashin kyautawa da suka ce an yi a tsawon lokacin da ake gudanar da rijistar masu zabe, inda kawancen ya nemi kotun tsarin milkin kasar da ta yi murabus.

Zaben Nijar

Shi ma shugaban kasar Mahamadou Issoufou baya ga kokarin dinke barakar da zaben kananan hukumomi ya nemi haddasawa tsakanin jam'iyun kasar inda ya umurci hukumar zabe da ta yi yadda 'yan siyasar suka bukata, ya kuma gayyato hukumar Koli ta Masu anfani da faransanci OIF da ta zo ta yi bincike kan rijistar da hukumar zaben ta yi kamar yadda 'yan siyasar suka bukata.

Wannan layi ne

Hukumar zabe ta CENI na ci gaba da shirye-shirye

Domin bai wa 'yan kasar da suka kai zabe damar gudanar da 'yancinsu na 'yan kasa ne hukumar zaben kasar CENI ta shirya rangadi a fadin kasar domin yi wa mabukata takardun haihuwa.

CENI ta ce za ta yi wannan takardun haihuwa ne daga watan Yulin 2018 zuwa watan Yunin 2020.

Yanzu haka dai CENI ta ce ta yi wa 1.703.402 takaradun haihuwa yayin da hukumar ta ce ta yi takardar shaidar aure 13. 412 daga ciki 8.402 sun je hannun masu su.

A wata ganawa da hukumar zaben kasar ta Nijar CENI ta yi da jam'iyyun siyasa ranar Alhamis din da ta gabata, shugaban Hukumar Maitre Issaka Sounna ya ce ga baki daya 'yan kasar da suka kai mizanin yin zabe su 7. 435. 364 ne suka yi rijista, inda mata suka kasance 4.087.145 sannan maza 3.348.219.

zaben Nijar

Har wa yau hukumar ta CENI ta ce daga cikin 9.751.462 din da shekarun su suka kai na yin zabe kwatankwacin kashi 76,25 cikin dari, kashi 55 cikin dari na mata ne suka yi rijistar yayin da maza suka kasance kashi 45.

Hukumar zaben kasar ta CENI ta kara da bayyana gyaran fuskar da ta yi wa jadawalin zaben kasar , yayin da zaben kananan hukumomi da ya kawo ja-in-ja tsakanin bangarorin siyasar kasar zai gudana ranar 13 ga watan Disambar 2020 , sauran zabubukan na nan a ranakun da hukumar ta zayyano tun farko.

Zaben shugaban kasa zagayen farko da na 'yan majalisar dokoki zai gudana ranar 27 ga watan Disambar wato mako biyu bayan na kananan hukumomi.

Karin labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne