Zaɓen Nijar: Abin da ya sa aka sauya ranakun zaɓen shugaban ƙasa da na ƙananan hukumomi

..

Asalin hoton, ceniniger

Bayan ƙorafe-ƙorafe da hukumar zaɓen Jamhuriyyar Nijar wato CENI ta sha daga 'yan siyasar ƙasar, a halin yanzu hukumar zaɓen ta bayyana cewa za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi kafin na shugaban ƙasa da na 'yan majalisa.

A ranar 13 ga watan Disambar 2020 ne hukumar ta bayyana cewa za a gudanar da zaɓen na ƙananan hukumomin.

Za a iya cewa jayayya tsakanin ɓangarorin siyasa a Jamhuriyyar Nijar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa ya sa Shugaban ƙasar Mahamadou Issoufou shiga cikin batun.

Shugaba Issoufoun dai ya gana da wakilai daga jam'iyyar MNSD Nasara Seini Umarou, da kuma shugaban gungun APR, ɗaya daga cikin abokan ƙawancen jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarraya kuma ɗaya daga cikin jam'iyyun da suka yi tsaya tsayin daka har har sai hukumar zaɓen ta shirya zaɓen ƙananan hukumomin kafin na shugaban kasa da na ƴan majalisa.

Bayan ganawar ce, shugaban kasar ya buƙaci hukumar zaben mai zaman kanta ta CENI da ta duba yiwuwar shirya wannan zaɓe da ƴan siyasar ke tayar da jijiyoyin wuya kamar yadda akasarin jam'iyyun siyasa suka yi fatan gani.

Bayan nazari da hukumar zaɓen ta yi, shi ne ta tsayar da ranar 13 ga watan na Disamba ta wannan shekara a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen na kananan hukumomi kafin na shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokoki da za a yi ranar 27 ga watan Disambar 2020.

To yaya masu wannan ra'ayi suka ji da matakin na hukumar zabe? Hambaly Dodo na gungun jam'iyyun 'yan ba ruwanmu cewa ya yi "in dai hukumar CENI ta bayar da himmar tsara wannan zaɓe, to lallai za ta biya wa mutane da yawa buƙatu, ganin cewa cikin shekara 10 ba a samu yin wannan zabe ba".

Ya bayyana cewa zaɓen yana da matuƙar muhimmanci ganin cewa ƙananan hukumomi su ke kula da karkara da talakawa da manoma da makiyaya.

Mace na kada kuri'ara a zaben Nijar
Getty
Wasu bayanai kan zaben Nijar na 2020

  • 147Yawan jam'iyyun siyasa a Nijar

  • 20Yawan 'yan takarar shugaban kasa a zaben 2020

  • Miliyan 21Yawan al'ummar kasar

  • Miliyan 9Yawan mutanen da suka yi rijistar zabe

Bayanai: Hukumar Zabe Ta Nijar

Ya ce idan aka yi zaben kananan hukumomi da kyau, hakan zai bayar da dama wurin shirin zaben ƴan majalisa da na shugaban ƙasa.

Ita kuma a nata bangaren jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarraya cewa ta yi ba ta da zaɓi game da ranakun wani zaɓe, kawai abin da ta sani, shirye take tare da fatan ganin hukumar zaɓen ta shirya ingantaccen zaɓen da kowa zai aminta da shi.

Wannan mataki na hukumar zaben ba karamin taimako zai yi ba wajen samo masalaha tsakanin bangarorin siyasa da batun zaɓen ƙananan hukumomin ke neman rarrabawa.

Zuwa yanzu dai Jamhuriyyar Nijar na da jam'iyyun siyasa 147 da yawan al'ummar ƙasar ya kai miliyan 21 da kuma 'yan ƙasar miliyan tara suka yi rijistar sunayensu domin kaɗa kuri'a a lokacin wannan zabe mai zuwa.