'Ana garkuwa da yaranmu da ke tafiya ci-rani Libiya daga Nijar'

Iyayen yara a Jamhuriyar Nijar na kokawa da matsanancin halin da 'ya'yansu matasa ke shiga a kokarin tafiya cirani a wasu kasashen Afirka.
Jihar Tahoua na daya daga cikin jihohin Nijar da matasan yankin ke fita ketare don neman kudi.
Sai dai mazauna yankin na kokawa kan halin da wadannan matasa kan samu kansu a ciki ta hanyar fadawa hannun miyagun mutanen da ke garkuwa da su.
Kasar Libya na cikin kasashen da matasa suka fi mayar da hankali wajen tururuwar zuwa don neman aiki.

Asalin hoton, SOS MEDITERRANEE
Wasu rahotanni na cewa iyaye da 'yan uwa na ta sayar da gonakinsu don aikewa da kudin fanso yaransu da aka sace.
Wani tsohon dan ci rani mazaunin garin Affala, Malam Haruna ya shaida wa BBC cewa galibin kasashen da ake zuwa cirani sun hada da Gabon da Libya da Senegal.
Ya ce matsalolin yunwa ke tilasta musu tafiya ci-rani, kuma abin takaici idan an kama mutum sai dai iyaye ko 'yan uwa su sayar da gonaki wajen ceto su.
''Mun sayar da gonakinmu ko kwanan nan an sayar da wata gona miliyan daya da jaka dari na Cefa aka aika kudin Libya don yin ceto.''
''Iyaye a Jamhuriyar Nijar sun nuna takaicinsu da halin galaibaita da yaransu matasa ke shiga a kokarin samar wa kansu abin rufin asiri.''
Malam Haruna ya ce ''ko da sun ce kar yaransu su zauna ba sa yarda, diyanmu mata kawai ke zama da mu shi ya sa su muke mayar da su makaranta''.
Yanzu haka muna noman rani mu iyaye ke yi saboda garin babu matasa.

Karin bayani
Jamhuriyar Nijar na cikin kasashen Afirka da ake fama da matsalar 'yan cirani da ke ratsawa ta kasar zuwa Turai
Wannan dalili ya sanya a cikin shekarar da ta gabata kungiyar Tarayyar Turai, wato EU, ta ba wa kasar kudi fiye da dala 600 domin dakile kwararar 'yan ci-rani.
Yankin Agadez mai yawan hamada dai ya zamo wata kafa ta bakin haure da ke bi domin ketarawa zuwa Libya kafin daga bisani su karkare a nahiyar Turai.
Tarayyar ta Turai dai ta bai wa kasashe irin su Senegal da Ethiopia da Najeriya da Mali irin wadannan kudade wajen hana bakin hauren kwarara.
Hakan ne ya sa aka samu raguwar hanyoyin da bakin hauren ke bi daga dubu 70 zuwa 2,000, a watan Nuwamban da ya gabata.
Hukumomi a Nijar sun yi alwashin yakar al'amarin kan jiki-kan-karfi duk da cewa ba su ambaci kudin da Tarayyar Turan ta ba su ba.












