Yadda aka kama muggan makamai a Katsinar Maradi da ke Nijar

bindiga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana yawan kai hare-hare da muggan makamai arewacin Najeriya da Nijar

Hukumomi a jihar Katsinar Maradi ta Jamhuriyyar Nijar sun yi karin bayani game da wasu dumbin makamai da hukumar tsaro ta Jandarmeri ta kama a karamar hukumar Gidan Roudji a ranar Litinin 6 ga watan Yuli.

Wata sanarwa daga hukumomin yankin suka ce a lokacin da gwamnan jihar ta Maradi Malam Zakari Oumarou ya ziyarci wurin a ranar Juma'a an gabatar masa da dumbin makaman da aka kama.

Makaman dai sun hada da bindiga samfurin AK-47 21 da madaukin albarusai 26 da alburusai 6,124 da tsabar kudi naira 309,000, da kuma babur daya.

An dai shiga da wadannan makamai ne daga arewacin Nijar a cikin wata motar shiga yashi. To sai dai dreban motar ya tsere da motar da ta dauko wadannan kaya.

Amma an kama mutum biyu daga cikin wadanda ke dauke da kayan da kuma wani mutum na uku da aka ajiye makaman a gidansa.

Gwamnar jihar Maradi Zakari Oumarou ya sanar da cewa wadannan makamai irin su ne ake amfani da su wajen kai hare-hare a arewacin Najeriya da kuma yankin kudancin jihar Katsinar Maradi.

A wannan shekara ta 2020 'yan bindiga sun yi awon gaba da dabbobi kimanin 50 000 a yayin da mutum 30 suka rasa rayukansu, wasu hamsin din kuma aka yi garkuwa da su sai da aka biya kudin fansa.

Bindigogi
Getty
Abubuwan da aka kama a Katsinar Maradi

  • 309,000Tsabar kudin da aka samu

  • 6,124Albarusai

  • 26Madaukin albarusai

  • 21AK-47

Source: Malam Zakari Oumarou