Donald Trump: Yayar shugaban Amurka ta ce ɗan uwan nata 'ba shi da mutunci'

Wata hirar sirri tsakanin babbar yayar Shugaba Trump Maryanne da 'yar ƙaninta ta bayyana, wanda a cikinta aka ji ta tana kakkausar sukar halayyar shugaban na Amurka.

Hirar ta ja hankulan mutane a Amurka da sauran sassan duniya saboda yadda dangantakar da Shugaba Trump ke da 'yan uwansa ta kusan taɓarɓarewa baki ɗaya.

A cikin faifan, Maryanne Trump -- wadda tsohuwar alkali ce -- ta kira shugaban Amurkar maras mutunci, wanda ya kasance maƙaryaci kuma maƙetaci.

Mary Trump, wata 'yar kanin baban Donald Trump ce ta naɗi hirar ce yayin da ta ke tattaunawa da innar tata.

A watan jiya Mary ta wallafa wani littafi da a cikinsa ta caccaki Mista Trump. Sunan littafin Too Much and Never Enough: How My Family Created the World's Most Dangerous Man, wato "Abu mai yawa wanda ba ya isarwa: Yadda iyalan gidanmu muka ƙirƙiro mutum mafi hatsari a duniya."

Mary Trump ta ce ta naɗi hirar ce a fakaice domin kare kanta - domin shugaba Trump na iya maka ta a gaban shari'a.

Ga wani cikin abubuwan da Maryanne ta ce game da ƙanin nata:

"Allah wadan sakonnin da yake aikawa a tiwita da yawan karyar da yake yi. Na san na saki baki na da yawa kin gane ko? Ga shi da saurin sauya gaskiyar abubuwan da suka faru. Ga ƙarya. Kash! Amma na san yana neman goyon bayan masoyansa ne. Ga kuma batun abubuwan da suke yi na raba ƙananan yara da iyayensu a kan iyakarmu!"

'Wani ne ya rubuta masa jarrabawar kammala sakandare'

Akwai kuma wani wuri da yayar ta Mista Trump ta shaida wa 'yar ƙanin mahaifin nasu Mary cewa Mista Trump yayi hayar wani mutum mai suna Joe Shapiro ne ya rubuta ma sa jarabawar kammala sakandare.

Maryanne ta ce: "Amma na san bai shiga kwaleji ba. Ya tafi makarantar Fordham na shekara guda ne kawai sai ya tafi jami'ar Pennsylvania, domin ya biya wani ya rubuta ma sa jarabawarsa."

A baya dai Maryanne ta riƙa goyon bayan ƙanin nata Donald kuma ta ce sun shaku matuƙa.

Ta ma taɓa bayar da wani labari na yadda ya riƙa kai ma ta ziyara a asibiti yayin da aka yi ma ta tiyata.

Mista Trump dai na fuskantar ƙalubalen da bai taɓa tsammani ba - daga batun ko yana biyan haraji zuwa na karya dokar zabe da yadda ake ta kama makusantarsa da aikata manyan laifuka.

Akwai kuma batun koma bayan tattalin arziki amma daɗin-daɗawa yawan mace-macen Amurkawa daga annobar korona na yi ma sa kutungwuila a wannan lokaci da zaben shugaban ƙasa ya kawo jiki.

Abokin hamayyarsa Joe Biden na jam'iyyar Democrat ya ba shi gagarumar rata a ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan.