Donald Trump ya yi kira a jinkirta zaɓen shugaban Amurka

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira a jinkirta zaben shugaban kasar wanda za a yi a watan Nuwamba.

Mr Trump ya ce karuwar da ake samu ta yin zabe ta hanyar aikewa da wasiku a gidan waya zai iya haifar da magudi da sakamakon zabe maras inganci.

Ya bayar da shawarar a jinkirta zaben har sai mutane sun samu damar kada kuri'a "a tsanake, cikin sirri da kuma kariya".

Babu wata shaida kwakkwara da ta gaskata ikirarin Mr Trump cewa zabe ta hanyar gidan aike wa da wasiku yana haifar da magudi sai dai da ma ya dade yana caccakar gudanar da zabe ta wannan hanya wacce ya ce tana kawo magudi.

Jihohin Amurka suna so su saukaka hanyar zabe ta aikewa da wasiku saboda annobar korona.

Me Trump ya ce?

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mr Trump ya ce "kada kuri'a ta hanyar gidan aikewa da wasiku" zai sa zaben watan Nuwamba ya zama "mafi rashin inganci kuma mai cike da magudi a tarihin zabuka" kuma hakan "babban abin kunya ne ga Amurka".

Ya bayyana cewa kada kuri'a ta wannan hanya ka iya haifar da kutse cikin harkokin zaben Amurka daga kasashen waje.

"Mambobin jam'iyyar [Democrats] sun yi bayani a kan tsoma bakin kasashen waje a harkokin zabe, amma suna sane cewa kada kuri'a ta hanyar gidan wasiku ita ce hanya mafi sauki ga kasashen waje su yi kutse cikin harkokin zabe," in ji shi.

A farkon watan nan, jihohin Amurka shida suka tsara gudanar da zabe wanda "dukkansa zai kasance ta gidan aikewa da wasiku" a watan Nuwamba. Jihohin su ne: California, Utah, Hawaii, Colorado, Oregon da kuma Washington.

A watan Yuni jihar New York ta kyale masu kada kuri'a su yi zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democrat ta hanyar aikewa da wasiku a gidan waya. Sai dai an fuskanci tsaiko wajen kidaya kuri'un.