Zaɓen Amurka Na 2020: Obama da Trump na yi wa juna gori

Barack Obama ya zargi Donald Trump da ɗaukar mulkin Amurka kamar ''dandalin wasa kwaikwayo'', a kalaman caccaka da ya yi amfani da su kan shugaban a taron jam'iyyar Democratic na ƙasa.

Tsohon shugaban Amurkan ya ce wanda ya gaje shi daga jam'iyyar Republican ''ya kasa samun ci gaba a aiki saboda gazawarsa''.

A fadar White House, Mista Trump ya mayar da martani tare da cewa an zabe shi ne saboda ''mummunan yanayin fargaba'' da Mista Obama ya jefa Amurkawa a ciki.

A rana ta uku ta taron Democratic, Kamala Harris ta amince da zaɓin mataimakiyar shugaban kasa da aka yi mata.

Rana ta hudu za ta kasance ta ƙarshen taron kuma mutumin da Democratic ta tsayar a matsayin ɗan takararta Joe Bide zai gabatar da jawabi a ranar Alhamis.

Biden da Harris za su kalubalanci ƙwatar White House daga hannun Shugaba Trump da mataimakinsa Mike Pence a zaɓen 3 ga watan Nuwamba.

Annobar cutar korona ta tilasta wa Democrats watsi da salonta na haɗa cikowar mutane cikin salo na biki da hayaniya da shewa inda a wannan karon taron ya kasance na intanet da naɗar wasu daga cikin bayanai ko jawabai kai tsaye.

Me Obama ya ce?

A daren Laraba, Mista Obama ya yi amfani da kalmomin suka mafi tsauri a kan Mista Trump, a maganganun da ya yi kai tsaye daga gidan tarihin adana kayan tarihin juyin-juya halin Amurka a Philadelphia.

Ya ce: ''Mr Trump ba shi da sha'awar aiki bisa cancanta. Ba shi da ra'ayin samar da maslaha.

''Ba shi da niyyar amfani da ƙarfin ikon ofishinsa wajen taimako face abin da ya shafi kansa da abokansa.

''Ba shi da ra'ayin girmama kujerar shugaban ƙasa a matsayin wani abu mai muhimmanci sama da wasan kwaikwayon da yake ganin zai taimaka masa wajen janyo hankali wanda yake kwaɗaitawa kansa.''

Ya ce abubuwan da muke girbewa na shugabancin Trump sun kasance ''yanayi mafi muni a tarihi, martaba da ƙimar da muke da ita a duniya ta disashe, sannan cibiyoyin dimokradiyarmu na fuskantar gagarumar barazanar da ba a taba gani ba.''

Tsohon shugaban ya nuna takacinsa kan abin da ya bayyana '' kalamai masu dabaibayi, rashin kirki da ƙarerayi da labaran ƙazon kurege''.

''Kar ku kuskura ku ba su damar su ƙwace mulkinku,'' ya gargaɗi Amurkawa masu zabe.''Kar ku bari su ƙwace dimokraɗiyarku.''

Mista Obama ya karfafa wa masu zabe gwiwar cewa su zabi tsohon shugaban kasa, Mista Biden, cikin kwana 76 masu zuwa - cikin yabo da ambatar cewa ''abokina'' kuma ''ɗan uwana''.

A cewar kamfanin dillanci labarai na Associated Press, majiyoyi daga makusantan Mista Obama sun tabbatar yana goyon baya Mista Biden, sai dai yana nuna damuwa a kan matasa masu zaɓe da kuma masu amfani da wariyar launin fata wajen kaɗa ƙuri'arsu.

Tsohon shugaban Amurkan an san shi da kare mutuncinsa da ƙin cewa uffan a bainar jama'a kan magajinsa.

Sai dai Mista Obama shekaru hudu da suka gabata lokacin da yake mulki ya taba gargadin cewa '' cin mutunci ne gareshi'' idan Amurkawa suka zabi Mista Trump, wanda ke takarar a Republican kuma tsohon mai gabatar da shirin talabiji na The Apprentice.

Shugaban Amurka na 44 sannu a hankali na fitowa karara yana bayyana ra'ayinsa kan magajinsa yayin da yake kallon yadda yake daidaita martabarsa.

A daren Litinin a taron Democratic, Michelle Obama ta gabatar da jawabin suka cikin salo kan wanda ya gaji mijinta, ta bayyana shi a matsayin wanda ba shi da kwarewa wanda hakan ''ƙarara ya nuna a kansa''.

Kalamanta sun janyo ce-ce-kuce tsakanin Amurkawa da dama saboda matar shugaban kasa, mai ci ko tsoho, na taka tsan-tsan wajen tsokaci kan wasu fitintinun siyasa.

Wane martani Trump ya mayar?

A yayin wani taro manema labarai a Fadar White House ranar Laraba, an tambayi Mr Trump kan kalaman Obama.

"Na ga irin masifar da ya bar mana, da shirmen da ya dinga yi,'' in ji shugaban Amurkan.

''Kalli irin lalata abubuwa da ya yi, da irin yadda ya kasa taɓuka abin a zo a gani, shi wata irin masifa ce.

"Shugaba Obama bai yi aiki mai kyau ba, kuma na zama shugaban ƙasa ne don na gyara barnar da Obama da Biden suka yi.''

Ya ƙara da cewa: ''Ba su yi abin kirki ba a kujerunsu dalilin kenan da ya sa na zama shugaban ƙasa.''

A wani saƙon tuwita da ya biyo baya da Mista Trump ya wallafa ya ce: ''Sannunku da dawowa Barack da Hillary. Mu haɗu a filin daga!''

Ana sa ran shugaban zai amince da aniyar sake tsayawarsa takara a jam'iyyar Republican a Fadar White House mako mai zuwa yayin taron jam'iyyarsa.