Boko Haram a Borno: Ƙungiyar ta kai hari Kukawa ta hana mutane fita

boko haram

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Boko haram ta shafe shekara 10 tana kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya

Rahotanni daga jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari garin Kukawa tare da hana mutane fita daga cikinsa.

Har yanzu rundunar sojin ƙasar ba ta ce komai ba kan harin, wanda yake zuwa kwanaki kaɗan bayan da ɗaruruwan ƴan gudun hijira suka koma garin da zama.

Labarin harin ƙungiyar ya nuna yadda har yanzu suke da sauran karsashi duk da ƙoƙarin da sojojin ƙasar ke yi na murƙushe su.

Har yanzu babu wasu bayanai masu yawa kan abin da ke faruwa a Kukawa - wanda ba shi da nisa sosai da Tafkin Chadi.

Babu wayar salula a can - abin da ke tuna yadda rikicin da aka shafe shekara 10 ana yi ke shafar ci gaban yankin.

A makon da ya gabata ne ɗaruruwan ƴan gudun hijira da aka raba da muhallansu suka koma garin da zama - an shaida musu cewa a yanzu garin na cikin aminci.

Kusan mutum miliyan biyu rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a arewa maso gabashin Najeriya kuma Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi cewa har yanzu akwai sauran matsala saboda taimakon hukumomin jin ƙai ba ya iya kai wa ga rabin mutanen.