Mpape Crushed Rock: Wajen da 'yan Najeriya ke tururuwar zuwa yawon bude ido

Asalin hoton, Fatima Muhammad

Wurin fasa dutsen da aka yi watsi da shi a Najeriya ya zama sabon wurin shakatawar masu sha'awar yawon bude ido bayan wallafa hotunan wannan waje a shafukan sada zumunta a farkon wannan watan.
Yadda manyan duwatsu suka kewaye wurin, sannan mutane suna tattakawa da hangen sararin samaniya ga kuma 'yan ciyayi koraye da suka fito jikin duwatsu da dan tafki da ke tsakiya abin kayatarwa ne da ban sha'awa, sannan hotunan da aka rinka watsawa a shafukan tuwita a farkon watan Agusta mutane sun yi ta latsa alamar sha'awarsu, sama da dubu.
Kwanaki bayan wallafa hotunan wurin, da aka fi sani da Crushed Rock, a Mpape - yankin marasa karfi da ke wajen birnin Abuja - ya ga cikowar mutane.
Makada na kade-kaden nishadantarwa, masu abinci na hada-hadarsu, ga daruruwan mutane da ke daukar hotuna - da kuma makadan garaya da ganguna.

Asalin hoton, Fatima Muhammad
'Yan Najeriya ba masu sha'awar fita shakatawa a waje ba ne - yanayinsu akwai tsananin zafi a arewa sannan kudancin ma akwai zafi da yawan damuna.
Sai dai, akwai masu sha'awar hawa tsaunuka a Abuja da masu wayewar son fita shakatawa da kuma 'yan baki da ke shigowa birni.
Annobar cutar korona ta taka rawa wajen ingiza ko karfafa gwiwar matasan Najeriya masu matsakacin ƙarfi su je shatakawa a saman dutsen.
Dokar kulle ta hana mutane balaguro don haka wadannan duwatsu sun kasance sabon wurin da mutane ke zuwa saboda shakatawa da nishaɗi.

Asalin hoton, Fatima Muhammad
Yankunan kewayen Mpape, da ke nufin ''dutse'' a harshen Gbagyi, anan aka samo galibin duwatsu da aka yi amfani da su wajen fasalta Abuja daga karamin kauyen a shekarun 1980 zuwa babban birnin tarayyar Najeriya.
''An shafe sama da shekaru 10 ana fasa dutse a wannan wuri,'' a cewar mazaunin Mpape, Courage Ebenz wanda ya sha mamakin ganin yadda mutane ke tururuwar ziyartar yankin nasu.

Asalin hoton, Fatima Muhammad
Najeriya na da tarin albarkatu da kayatattun wuraren ban sha'awa, sai dai wannan wuri da mutane suka samar na da nasa abin jan hankalin - ya kasu kashi uku kuma kowanne na da nasa kayatarwar wajen hangen ruwan da ke kasa.
Masu yawon bude ido na iya bi ta hanyar da aka ware domin hawa da kafa, inda ciyayi suka kayatar gwanin son zama don shakatawa.

Asalin hoton, Fatima Muhammad
Yayin da kake tattakawa gwanin ban sha'awa kana karo da abubuwa da za su dauke maka hankali da kuma iya hango macizai ta gefen kasan gulbin.
Sai dai ana aike gargadi ka masu karfin halin da za su yi tunanin shiga ruwa da su yi hattara saboda akwai abubuwa masu hadari a cikin gulbin.

Asalin hoton, Fatima Muhammad
A cewar Abraham Adepelumi, masanin muhalli a Jami'ar Obafemi Awolowo, an samu wannan gulbi ne sakamakon fasa duwatsu da ke rike ruwan kasa.
''Idan aka fasa dutse, ruwan da ke cikin dutse na shiga matsi,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.
''Ba bakon abu ba ne, Mpape yanki ne da ake fasa duwatsu a Abuja da aka sha ganin motsin kasa, na baya-bayan nan a 2018.''

Karin labaran da zaku so karantawa:

Hukumar agajin gaggawa a birnin ta gargadi 'yan koyo da su guji hawa Dutsen Mpape, sai dai masu son nishadi da alama ba sa jin wannan gargadi.
''Ba mu san muna da irin wannan wurin ba a Najeriya kuma ina son ganin ko gaske ne,'' a cewar Elizabeth Okute, wacce ta ziyarci dutsen Mpape tare da kawayenta bayan ganin hotunan wajen a Facebook.
''Na yi mamakin akwai irin wadannan wuraren a Abuja kuma ina matukar kaunar abin da idona ya gane min,'' a cewar Ann Chukwuka.

Asalin hoton, Fatima Muhammad
Emeka Uko, wanda ya yi kuri da idanu yana kallon abin al'ajabi tare da abokansa, ya ce: ''Ina fatan mu dage domin ganin mun kare wannan wuri.''
Wannan shi ne abin da masu sa kai suka yi ta kokarin yi a ranar Asabar ɗin da ta gabata, inda suka rinka kwashe datti da robobin da aka watsar a kan dutsen tsawon makonni.

Asalin hoton, Fatima Muhammad
Sun raba kansu gida biyu, inda suka yi gasar ganin wane ne zai kwashe shara mafi yawa - da kuma sabunta shafukan sada zumunta kamar yadda suka je.
''Mutane da dama na ganin hakkinsu ne su killace wurin,'' kamar yadda Brandon Akume, wanda rukuninsu ya zo na biyu a gasar tsafttace kan dutsen, ya shaida wa BBC.
Wannan shi ne tunanin akasarin 'yan Najeriya a yanzu, a cewarsa.

Asalin hoton, Fatima Muhammad
Ya sauya tawaga tsakanin waɗanda suka je shakatawar, inda ya mika ledarsa ta zuba shara, da umartar mutane su zubar da dattin.
''Suna son su hallaka wurin, shi yasa na ware aikina daga cikin nasu,'' a cewarsa.
Hotuna daga Fatima Muhammad kalamai kuma na Nduka Orjinmo na BBC.










