Yadda ambaliyar ruwa a Abuja 'ta yi sanadin mutuwar matata da 'ya'yana'

Ambaliyar ruwa
Bayanan hoto, Sadiq Abdulhamid ya rasa matarsa da 'ya'yansa hudu sakamakon ambaliyar ruwa

Sadiq Abdulhamid, mai kimanin shekara 35, na cikin damuwa da alhini na rashin iyalansa da ambaliyar ruwa ta yi sanadinsu a Gini Gota, da ke Angwa Kaura a karamar hukumar Gwagwalada da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Tun da ya samu labarin, Sadiq bai daina kuka da kuma neman iyalansa a cikin ruwan da ya tafi da su ba saboda yana fatan ko da zai ga gawarsu.

Amma har yanzu babu wani bayani, abin da kansa Sadiq kuka da bacin rai kenan a kullum tun bayan da ruwan ya tafi da iyalansa.

Ya ce: "Sai da na fadi bayan da na samu labarin, kuma da wani zai ce mini haka zata faru da iyalina da na karyata shi."

"Ban taba tunanin matata da dana za su mutu su bar ni ba, kuma har ma ban yi musu jana'iza ba, saboda ko ba komai idan na ji kewarsu da na rinka zuwa kabarinsu ina musu addu", in ji Sadiq.

Ba wai bacin ran iyalansa sun mutu Sadiq ke ciki ba, a'a, rashin kasancewarsa a gida a lokacin da abin ya faru da ya kubutar da matarsa da 'ya'yansa hudu.

'Ya'yan Sadiq sun hadar da Abdullatif mai shekara 12, sai Latifat shekara 9, da Rahimat shekara 5 sai kuma Hamida jaririya 'yar watanni hudu.

Sun mutu ne a ranar Asabar 25 ga watan Yuli, 2020, bayan an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya haddasa ambaliyar ruwa a yankinsu.

Ya ce: "Na je wani kauye ne a Kogi domin na noma mana abincin da zamu ci ni da iyalaina saboda na rasa aikin da nake na gadi, da kudin da na tara na gadin na nayi na gina mana gidan da muke ciki ni da iyalaina wanda yanzu ruwa ya tafi da komai.

"Gani nake abin da ya faru kamar mafarki ne," in ji Sadiq.

Ambaliyar ruwa
Bayanan hoto, Yadda ambaliyar ruwa ta yiwa giri

Yadda Habibat matar Sadiq ta mutu

Habibat malamar makaranta ce a wata makaranta da ke garin.

Tun bayan da mijinta ya rasa aikinsa na gadi, ta ke aiki domin taimaka wa iyalansu da abin da take samu wanda bai wuce naira dubu goma ba.

Ba ta jima da haihuwa ba, tana jaririya 'yar wata hudu, an fara ruwan sama a cikin daren Asabar da misalin karfe uku, ba ta yi aune ba, wajen karfe shida ruwa fara bullowa ta rufin gidansu can sai ruwa ya ballae ya shigo gidansu.

Ta yi ta ihu tana kiran a kawo musu dauki domin taga gadon take kwance da wanda yaranta ke kwance ya fara yawo a saman ruwa, amma shiru ba bu wanda ya fito.

Can ta dauki jaririyar ta rungume a haka ruwa ya tafi dasu dukkansu wanda har yanzu ba a ga gawarsu ba.

Wani ganau, Abdulrazaq, ya ce yana ganin yadda ruwa ya tafi da su amma babu abin da zai iya yi ya taimaka musu.

Mutuwarta ta kada mutane da dama a garin, wata kawarta Charity ta bayyana ta a matsayin jajirtacciyar mace.

Cikin kuka, Charity ta shaida wa sashen BBC na Pidgin cewa ta yi rashin aminiya.

Gidaje da wuraren kasuwanci duk sun lalace

Ambaliyar ruwa

Fiye da gidaje talatin ambaliyar ruwan ta lalata, inda har yanzu jama'ar garin ke kirga irin asarar da suka yi.

Afiniki Auta tana da 'ya'ya shida, kuma kusan ta rasa komai nata, to amma ita da 'ya'yanta da mijinta sun kubuta daga ambaliyar ruwan.

Mrs Jacob Francisca, bazawara ce kuma tela ce, inda ta ke amfani da sana'arta wajen kula da 'ya'yanta wanda mijinta ya mutu ya bari, yanzu gidanta da kuma shagonta duk ruwa ya cinye.

Ambaliyar ruwa

Mafi yawancin mutanen wannan gari ambaliyar ruwan ta shafe su, domin da yawansu suna tsaye ba su da wajen zama ballantana wajen kwanciya.

Rashin gini mai inganci na haddasa ambaliyar ruwa

Ambaliyar ruwa

Giri Gota gari ne da ke da yawan jama'a marassa karfi da kuma wadanda ke aiki.

Mafi yawa daga cikin mutanen wannan gari sun gina gidajensu ne domin su zauna tare da iyalansu saboda ba za su iya biyan kudin haya ba a cikin garin Abuja.

Shugaban al'umma a wannan gari, Bako Ndazhaga ya ce an samu ambaliyar ruwa a wannan yanki ba kuma wani ya haddasa ba.

To sai ya danganta abin da cewa kwatar da kamfanin Dantata and Sawoe ya gina karama ce ita ta haddasa ambaliyar ruwan.

Ya ce maimakon kamfanin ya gina musu gada da kuma kwalbati babba wadda ruwa zai iya wucewa duk yawansa, sai aka gina musu karamar kwata.

Shugaban al'ummar ya ce a shekarar 2010 ne aka bai wa kamfanin na Dangote anda Sawoe kwangilar amma ba a yi musu aikin da ya kamata ba.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta kasa, Malam Abbas Idris, ya ce har yanzu suna kokari domin gano gawar iyalan Sadiq, ko da yake an gano gawar babbar dansa kuma tuni aka binne shi.

Ya ce ambaliyar ruwa ta fi kamari a yankunan kananan hukumomin Abuja hudu wato AMAC da Gwagwalada da Kuje da kuma Kwali.

Dangane da kokarin da gwamnati ke yi wajen kiyaye afkuwar ambaliyar ruwa, ya ce suna kokari domin gano duk wuraren da ke da yiwuwar samun ambaliyar ta yadda za a tabbatar da dakile afkuwar hakan.