Saurayi ya kashe kansa a Kano saboda budurwa ta ƙi aurensa

.

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar 'yan sanda ta Jihar Kano ta ce ta fara bincike game da wani saurayi mai shekara 22 da ake zargin ya kashe kansa ranar Alhamis sakamakon buduwarsa ta ƙi aurensa.

Mai magana da yawun rundunar DSP Haruna Abdullahi ya shaida wa BBC cewa sun karɓi rahoto cewa Ashiru Musa mazaunin unguwar Danrimi ya caka wa kansa wuƙa saboda bai samu auren wata yarinya ba mai suna Fatima.

Musa Sani, mahaifin Ashiru, shi ne ya kai wa 'yan sanda rahoto, a cewar rundunar, kuma ya mutu ne bayan 'yan sanda sun kai shi Asibitin Murtala da ke birnin Kano.

DSP Haruna ya ce sun karɓi rahoton da misalin ƙarfe 9:00 na dare.