Budurwa ta je neman aure gidan su saurayi don kare hakkin mata

Tariqul Islam (right) and bride Khadiza Akter Khushi pose for a photo during their wedding in Meherpur

Asalin hoton, Ujjwal Masud

Bayanan hoto, Khadiza Akter Khushi ta auri Tariqul Islam bayan karya tsohuwar al'ada

A lokacin da Khadiza Akter Khushi ta jagoranci fiye da mutum dari zuwa gidan wanda zai zama angonta, ba ta yi hakan don wadanda suka ziyarci bikinta ba kawai.

Ta yi ne don matan kasar Bangladesh inda take sa ran za subi sahunta.

Zuwan nata gidan su saurayin shi ne karo na farko da ake tunanin ya sauya al'adar da ake yi ta daruruwan shekaru, inda aka saba maza ne ke zuwa gidajen amarensu a ranar biki.

''Idan dai har maza za su je neman auren mata, to me zai hana matan ma su yi?'' Ta tambayi wakiliyar BBC Bengali kwanaki kadan bayan labarin aurensu da Tariqul Islam ya yadu kamar wutar daji.

Sai dai labarin auren ya dauki fuska biyu inda ya bai wa wasu kwarin gwiwa ya kuma bai wa wasu mamaki matuka. Wani mutum kuwa, bayar da shawarar cewa a jefi ma'auratan da kuma iyalansu da silifas.

Khadiza da mijinta dai suna ganin abin da suka yi din daidai ne.

Ta shaida wa BBC cewa "Al'ada ba ita ce matsalar ba a wannan badakalar, batu ne na hakkin mata. A yau don mace ta je neman auren namiji, babu wanda aka cutar.''

Ta kuma ce ''Sai dai ma, yin hakan zai rage cin zarafin mata da kuma kara musu kima da daraja. Babu wanda zai fi wani. Ko kuma ba za a fifita wani kan wani ba.''

relatives of groom Tariqul Islam welcome bride Khadiza Akter Khushi (C) with a floral wreath as she arrives to groom"s house during their wedding in Meherpur

Asalin hoton, AFP

Ma'auratan na da masaniya kan kin wannan aure da suka yi a yankin wata karkara da ke kusa da iyakar Indiya a makon da ya gabata.

Hasali ma wasu daga cikin danginsu ba su mai da hankali da fari a kan batun ba.

Amma Tariqul mai shekara 27 ya ce sun dai yi sa'a abu ya tabbata. Duk da cewa babu wani abu da suka yi wanda ba dai-dai ba.

Sabon ango da amaryar sun ce, mutane da dama na daura aure a kotu, wasu kuma a masallaci. Mu an yi mana aure bisa koyarwar addini.

An samu Kazi wato rajistar aure da kuma shaidu. Haka aka mana rajistar aurenmu. Haka ka'idojin auren suke, kuma abunda muka yi Kenan.

Ba mu damu da yadda mutane suka dauki aurenmu ba ko kuma abunda za su ce. Tunanin wasu mutane akan auren zai iya zama wani iri, kowa dai nada iko akan ra'ayinsa.

Presentational grey line

Al'adun da na neman rikidewa

daga Sanjana Chowdhury, BBC Bengali

Bisa al'ada dai anan, ango da danginsa ne ke zuwa gidan su amarya inda za a daura aure a kuma yi shagulgulan biki, bayan nan ne amarya za ta yi sallama da nata dangin sannan ta wuce gidan mijinta.

Haka ake yi tun a zamanin da.

Sai dai a Meherpur, wani yanki da ke yammacin Bangladesh, wani abu daban ya faru: anan, amaryar ce da danginta suka kai kansu gidan ango domin a daura musu aure, bayan an gama sai angon ya koma gidansu amaryarsa da zama.

Fa'idar wannan abu ko akasinsa na da yawa, ga maza da yawa, za su dauki yin hakan a matsayin abun kunya da kuma rage musu daraja da kima. Wasu kuma na ganin shi a matsayin abunda ma bai kamata ba.

Wannan ba zai taba faruwa a biranen Bangladesh ba, ballantana a dan karamin kauye. Wadannan ma'aurata dai sun fara gudanar da rayuwar aurensu inda suka nuna bajinta.

Presentational grey line

Duk da nuna karfin halinsu, matakin da suka dauka din ba karami ba ne.

Bangladesh ta yi kokari matuka a shekarun baya-bayan nan wajen kokarin kawo daidaito tsakanin mata da maza, sannan kuma kasar na mataki na sama a kudancin yankin Asia idan aka zo batu na daidaito tsakanin maza da mata in ji kungiyar tattaunawa kan tattalin arziki na duniya.

Sai dai, akwai sauran rina a kaba. Mutuwar Nusrat Jahan Rafi wadda ke da shekara 19, dai-dai da shekarar amarya Khadiza, ya zama kanun labarai a sassan duniya. Inda ake zargin cewa an kona ta da ranta bayan ta kai karar shugaban makarantarta da ya yi kokarin cin zarafinta.

Daga bisani, Majalisar Dinkin Duniya ta ce a sassan duniya, kaso biyu cikin uku na mata da suka yi aure na fuskantar barazana a wajen iyayensu, inda rabi kuma a ciki ke kai karar ana cin zarafin su a shekarar da ta gabata.

A yayin kuma da matsayin mata ke kara yawa a bangarori kamar na ilimi da dokokin aure a kasashen da musulmai suka fi yawa, kungiyoyi na kare hakkin mata na sukar su, suna cewa wadannan sun wuce iyakar su sun kuma zama saniyar ware.

Presentational grey line

Sai a watan da ya gabata ne babbar kotu ta yanke cewar yanzu mata ba sai sun bayyana cewa ko sun taba sanin da na miji ba a wajen cika fom din aure, alhalin su mazan ba sai sun yi hakan ba.

Tariqul da Khadija na da yakinin cewa aurensu zai zama wani karin mataki na hakika wajen kawo daidaito tsakanin maza da mata.

Na tabbata aurenmu zai aika da sakon cewa mata na iya yin duk abunda namiji zai iya, kamar yadda Tariqul ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Kuma ko da bai kasance hakan ba, za su kasance cikin farin ciki da zabin da suka yi wa kansu.

Mun nishadantu sosai a wajen bikin in ji Khadiza.