Biranya ta haihu bayan tsarin iyalin da aka yi mata ya gaza aiki

Asalin hoton, Ngamba Island Chimpanzee Sanctuary
Wata biranya da ke rayuwa a wurin da ake killace birrai ta haihu ba tare da ta shirya wa hakan ba, bayan da aka dasa mata wani maganin tsarin iyali, kamar yadda jami'ai suka shaida wa BBC.
Hukumar kula da wurin da ake killace birran na Ngamba Island Chimpanzee Sanctuary da ke Tafkin Victoria sun kadu bayan gano biranyar na da ciki, sannan sun ce an gudanar da gwaje-gwajen kwayoyin halitta don gano wanda ya yi mata cikin.
Biranyar, wacce ake kira Natasha, za ta kai shekara 29. An ceto ta ne daga Arua a yammacin kasar kusan shekara 21 da suka gabata.
Babban mai kula da wajen killace birran ya ce suna kokarin hana dabbobin haihuwa ne saboda ba su da isassun abubuwan kula da jariran da za a haifa.
Wani likitan dabbobi Titus Mukungu ya shaida wa BBC cewa "Ana iya yi wa birrai tsarin iyali kamar yadda ake yi wa mutane don hana su daukar ciki.
"Ana hakan ne don a hana dabbobin yaduwa a wajen da ya kasance an yi shi ne kawai don kula da marayun dabbobi ko wadanda aka tsinta suna gararamba."
Ya ce a cikin shekara 20 din da suka gabata jarirai hudu kawai aka haifa a wajen, don haka magungunan tsarin iyalin su kan yi aiki.
Haihuwar da biranyar ta yi ranar 5 ga watan Satumba ya sa yawan birran da suke wajen ya kai 50.
Wata kungiyar masu kula da muhalli a Uganda ta roki mutane su zabar wa jaririyar biranyar suna.











