Dandaka 'za ta kawo karshen fyade'

Sarki Goodwill Zwelithini

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarki Goodwill Zwelithini ya fi kowanne sarki karfin fada-a-ji a Afirka ta kudu

Basaraken kabilar Zulu da ke Afirka ta Kudu Sarki Goodwill Zwelithini ya yi kira da a dandake duk mutumin da aka samu da laifin yin fyade.

Jaridar da ake wallafawa a shafin intanet the IOL ta ambato sarkin yana shaida wa talakawansa lokacin wani biki ranar Talata cewa "hakan zai kawo karshen wannan mugunyar ta'ada... ya kamata a yi dandakar ta yadda dukkan duniya za ta fahimci cewa masarautar Zulu ba ta maraba da wannan abin kunya."

"Maza irin mu ne za su yi dandakar", in ji basaraken.

Ya yi wadannan kalamai ne a yayin da rahotanni ke cewa ana samun karuwar yi wa mata fyade a Afirka ta kudu.

Lokacin da yake jawabi ga 'yan majalisar dokokin kasar makon jiya, Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce alkaluman masu yi wa mata fyade tamkar na kasar da ta shiga yaki ne.

An yi wa fiye da mutum 41,000 fyade a Afirka ta kudu daga watan Afrilun 2018. Hakan na nufin ana yi wa mutum daya fyade a duk minti 15.

IOL ya ambato Sarki Goodwill yana cewa: "Tun da dai muna yin kaciya, to yanzu ya kamata mu matsa gaba zuwa yin dandaka. Za mu yi haka ne domin karrama Sarki Shaka wanda ya kaddamar da dokokin da kasar nan ke mutuntawa."

An ambato wani mai fafutukar kare hakkin mata na kungiyar Sonke Gender Justice yana cewa "daukar irin wannan mataki kan mutanen da ke yi wa mata fyade ba zai taba magance matsalar ba".

Sarkin ba shi da mukami na siyasa amma yana da matukar karfin fada-a-ji a Afirka ta kudu.