An samu gawar saurayi da budurwa tsirara a Kano

'Yan sanda

Asalin hoton, Getty Images

'Yan sanda a Najeriya sun tabbatar da samun gawar wani saurayi da wata budurwa tsirara a dakin girki a wani gida da ke wata unguwa a jihar Kano.

Al'amarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren ranar Laraba.

'Yan sandan sun ce babu tabbacin dalilin mutuwar tasu, amma sun mika gawar zuwa asibiti don gudanar da bincike kan abin da ya haddasa mutuwar tasu.

Sai dai wasu daga cikin mazauna unguwar ta Badawa da abin ya faru sun bayyana cewar gidan da masoyan biyu suka mutu ba gidansu budurwar ba ne.

Wasu rahotanni na cewa kwanaki kadan ya rage a daura musu aure.

Amma iyayen namijin sun ce bisa ga yadda suka samu labarin, hayakin inji ne ya yi sanadiyar mutuwarsu.