An kama mutumin da yake 'tsafi da sassan jikin matansa a Katsina'

Rundunar 'yan sanda ta ce tana bincike

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar 'yan sanda a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta kama wani magidanci da ta zarga da wulakantawa da kuma cin zarafin matansa biyu.

Mutumin mai suna Sama'ila Musa, wanda bai wuce shekara talatin da haihuwa ba, ya daure matan nasa da sarka yayin da yake azabtar da su.

Sama'ila na zaune a wani kauye mai suna 'Yan na Bayye da ke karamar hukumar Rimi a jihar katsina.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar SP Gambo Isah, ya shaida wa BBC cewa, "Matashin ya daure matan nasa biyu ne a gidansa bayan ya saka musu sarka ya daure musu kafafuwa, sannan kuma yake wasu abubuwa irin na tsafi da matan."

Bayan samun labarin abinda ke faruwa a gidan matashin, babban jami'in dan sanda a karamar hukumar ta Rimi shi da kansa ya je gidan matashin ya gane wa idonsa abinda ke faruwa.

"Matan na sa sun yi bayanin cewa a wajen da aka daure su suke kashi da fitsari, lamarin da ya sa rundunar 'yan sandan ta ce akwai yiwuwar yana abubuwa ne na tsafi kuma ba mamaki yan cikin kungiyar asiri," a cewar rundunar 'yan sandan.

Matan matashin, sun kuma shaida wa 'yan sandan cewa, mijin na su ya yanke musu gashin kansu inda ya kai cikin wani akwati yana tsafi da shi.

Kazalika sun ce a wasu lokutan ya kan yanke musu farce ya daka sannan ya barbada musu a cikin abinci su ci.

Rundunar 'yan sandan ta ce ta ga shaidar duka sosai a jikin matan, kuma bulalar da suka gani yana dukan matan na sa da ita ko jaki ba za a daka da ita ba.

SP Gambo Isah ya kara da cewa, "Dubun Sama'ila ta cika ne bayan da mahaifiyar daya daga cikin matan ta je gidan don ganin 'yar ta, sai ya hana ta shiga.

"Tayi-tayi domin ya bar ta ta shiga ya ki, sai ta lura da cewa gidan ma a kulle yake.

"Daga nan ne sai ta garzaya zuwa ofishin 'yan sanda da ke kauyen ta sanar da su, a nan ne aka zo aka ga tarar da halin da matan ke ciki."

Yanzu haka dai an kai matan asibi an duba lafiyarsu, an kuma kira iyayensu an mika su a hannunsu.

Shi kuwa Sama'ila, yana tsare a hannun 'yan sandan jihar inda da zarar an kammala bincike za a gurfanar da shi gaban kuliya.