Kenya: 'Yan sanda sun yi wa wata mata tsirara don tabbatar da jinsinta

Bus din kabu-kabu a Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane kan layi suna shiga bus a Kenya

Wata mata kwandastar motar bas a Kenya wacce ke da gemu ta bayyana yadda 'yan sanda suka sa ta ta yi tsirara a ofishinsu domin tabbatar da ko ita mace ce.

Theresia Mumbi ta shaida wa BBC Swahili cewa 'yan sanda masu ba da hannu a babban birnin Nairobi, sun kama ta, tare da wasu mata sun kai su caji ofis.

Ta ce: "jami'an 'yan sanda biyu sun same ni, suka ce in tube kayana. Suka duba ni. Ban tabbatar da abinda suka gani ba, sai suka ce in mayar da kayana, in koma bayan kanta."

Ta ce, har yanzu ina tuna kamen da aka yi a watan Yulin 2018 kan bayanan shaida. Ta nuna takardunta sai aka kyaleta ta tafi.

Irin haka ya sanya Misis Mumbi zama wata jagorar mata irin ta, masu yanayin halitta kamar na maza, sa'annan a yanzu ta bayar da labarinta domin wayar da kan mata irin ta da karfafa masu gwiwa wajen buda murya idan aka muzguna musu.

An samu Mumbi da rashin daidaituwar halitta a jiki, wanda hakan ya sanya gemu ke fito mata.

A matsayinta na matashiya, tana yawan aske gemunta har ya kai ga fatarta na kuraje.

"A shekarun baya, na dakatar da aske gemuna a wani lokaci saboda kurajen da ke fesowa a fatata ya zame mini matsala", in ji Mumbi.

Da gemun ya girma, sai ta fara boyewa daga shiga cikin jama'a, ta zabi ta je sayayya da daddare.

Shiga wani yanayin rayuwa ya sanya ta zama kwandastar bas, domin samun abun dogaro da kai.

A yayin da take aikinta, ta kan hadu da wasu mata masu irin halittarta, take kuma karfafa musu gwiwa.

Tana cikin wata kungiyar mata masu gemu ta Kenya, sa'annan a lokacin taronsu, ta kan yi wa matasan mata magana.