Yadda 'yan sanda suka ritsa 'yan fashi a banki a Abuja

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta dakile yunkurin wasu 'yan fashi da suka yi na far wa reshen bankin First Bank Plc a Abuja babban birnin kasar a ranar Asabar.
Sai dai rahotanni na cewa aikin hadin gwiwa ne tsakanin 'yan sanda da kuma sojoji, inda suka harbe daya daga cikinsu sannan suka kama wasu hudu a harabar ginin bankin da ke Mpape a Abuja.
Jami'an tsaron sun zagaye ginin bankin ne kuma suka rutsa 'yan fashin a ciki na tsawon sa'o'i da dama.
BBC ta yi yunkurin jin ta bakin rundunar 'yan sandan birnin na Abuja amma abin ya ci tura.
Wasu hotuna da bidiyo da suka karade shafukan sada zumunta sun nuna yadda 'yan sandan suka kama wasu daga cikin 'yan fashin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Kazalika an ga mutane suna murna bayan namijin kokarin da 'yan sandan suka yi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Hakan ya sa Atiku Abubakar, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na watan Fabarairu da ya gabata, ya ce yana alfahari da aikin jami'an tsaron har ma ya tafa masu.
"Ina alfahari da namijin kokarin da 'yan sanda da sojojin Najeriya suka yi na dakile wannan fashi. Ina fatan tsaro zai ci gaba da inganta a sabuwar shekarar da za mu shiga," in ji Atiku.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3