Haƙar ma'adinai a Niger: 'Na rasa 'ya'yana uku saboda karya doka'

E say im no still dey suffer di pain
    • Marubuci, Dooshima Abu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin, Abuja

Wani mutum mai suna Nuhu da ke zaune a ƙauyen Shikira na jihar Naija a arewacin Najeriya na cikin jimami, shekara huɗu bayan gubar dalma ta kashe 'ya'yansa uku.

Wata rana ya tashi daga barci, sai ya ga 'yarsa ta farko na cikin wani hali na rashin lafiya, farko cikinta ne ke ciwo, sai ta fara farfaɗiya, ko da aka kai ta wani asibiti, sai Allah ya yi mata cikawa.

Nuhu bai gama dawowa daidai ba sai kuma 'yarsa ta biyu ta fara irin ciwon da ta farko ta yi - ba da daɗewa ba sai ta mutu haka ma ta ukun.

"Na ji zafi matuƙa da yara na har uku suka mutu a kan idona", in ji Nuhu.

"Duk lokacin da na tuna yadda suka mutu da kuma irin wahalar da suka sha, sai na fara kuka."

Yaran Hannatu biyu sun mutu
Bayanan hoto, Yaran Hannatu biyu sun mutu

Yaran Nuhu na daga cikin wasu ƙananan yara 28 da suka mutu a ƙauyen Shikira a 2015.

Ƙasar ƙauyen na ɗauke da guba sakamakon haƙar ma'adinai da ake yi ciki kuwa har da gubar dalma.

A farko, dabbobinsu ne suka fara mutuwa, kafin daga bisani kuma matsalar ta shafi yaransu.

Na dis time di causee lead poison for community

Wani mai suna Aliyu a ƙauyen shi ma ya rasa ɗansa, ya bayyana cewa mutanen ƙauyen na tunani kamar mayu ne suka kama yaron.

Amma daga baya sun gane cewa yadda suke haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, kuma ba tare da kulawa ba ne ya jawo musu hakan.

Abin gaba ɗaya ya shafi jama'ar ƙauyen, kuma shekara huɗu bayan faruwar hakan har yanzu suna cikin tashin hankali.

Dis method dey beta pass dry milling

Me ya sa ake yawan haƙar ma'adina ba bisa ƙa'ida ba a Najeriya

Har yanzu babu wani ci gaban a zo a gani a ɓangaren ayyukan haƙar ma'adinai a Najeriya.

Akasarin ma'adinan da ake haƙowa a ƙasar musamman a arewacin Najeriya masu haƙar ma'adinai na gargajiya ne ke yin aikin.

Lamarin ya jawo gurɓatar muhalli da kuma ƙalubale ga lafiyar al'ummar yankin.

Akwai sama da mutum dubu 500 da ke haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a Najeriya.

A shekarar 2010, an samu matsala matuƙa a jihar Zamfara inda yara 400 suka mutu, sai kuma a 2013, yawan ya ƙaru zuwa 700.

A 2015 kuma, sai kusan irin hakan ta faru a ƙauyen Shikira, har yanzu kuma 'yan ƙauyen na cikin jimami.

Pikin dem fit inhale di dust

Asalin hoton, Empics

Wane mataki gwamnati ta ɗauka don magance haka?

A yunƙurin gwamnatin ƙasar na faɗaɗa tattalin arizƙinta da kuma juya akalarta daga man fetur, gwamnatin ƙasar ta yanke shawarar karkata hankali ga ɓangaren haƙar ma'adinai.

Gwamnatin ta buƙaci masu haƙar ma'adinan da su haɗa ƙungiya wanda hakan zai sa hukumomi su iya tallafa musu.

most di young boys no dey sick again

Dakta Magaji, malami a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya bayyana cewa gwamnati ba ta mayar da hankali ba wajen hana haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.

Ya bayyana cewa gwamnatin ba ta da wani tsari a kimiyyance da za ta jawo hankulan masu zuba jari zuwa harkar.

many of dem di make between 10-50 thousand everi moonth

Ina mafita?

A lokacin da wannan mummunan lamari ya faru a ƙauyen Shikira, gwamnatin ƙasar ƙarƙashin ma'aikatar lafiya ta ɗauki matakin kawar da guba da kuma lalatatun sinadaren da ke kawo matsala a ƙauyen.

Ma'aikatar lafiyar ta bayar da magani ga sauran yaran garin, kuma ta koya wa jama'ar garin hanyoyin da za su bi wajen haƙo ma'adinan ba tare da sun jefa rayukansu cikin haɗari ba.

Ma'aikatar ta shaida wa masu haƙar ma'adinan da kada su rinƙa kawo kayan da suka haƙa gidajensu, an kuma koya musu yadda za su rinƙa tsaftace jikin su.

Many of di pikin dey smile

Ɗaya daga cikin likitocin ma'aikatar lafiya Dakta Simba Tirima ya bayyana cewa dabarun da aka koya wa masu haƙar ma'adinan ya sa yawan gubar da ke cikin ƙasa ta ragu da kuma ta cikin jinin 'yan garin.

Shekaru huɗu bayan wakiliyar BBC Dooshima Abu ta ziyarci ƙauyen ,jama'ar ƙauyen sun shaida mata cewa yaransu sun daina mutuwa sakamakon dabarun da aka koya musu na haƙar ma'adinai.