Zaɓen Belarus: Masu zanga-zanga sun yi wa shugaban ƙasa ihu

Asalin hoton, Reuters
Ma'aikata sun yi ta yi wa shugaban ƙasar Belarus Alexander Lukashenko ihu a yayin da ya kai ziyara wata ma'aikata yayin da mutane ke sake yin fushi da shi kan aben da aka gudanar mai cike da ruɗani.
Ma'aikata sun yi ta yin ihun ''ka tafi'' ga shugaban Belarus da ya daɗe a kan mulki a yayin da ya kafe cewa ba zai bari a yi sabon zaɓ ba bayan da ake zargin wanda aka yi na cike da maguɗi.
An fara yahjin aiki a ƙasar inda har gidan talbijin mallakin gwamnati ya bi sahu, har ma'aikata suka yi tafiyarsu a ranar Litinin.
Ƴar takarar jam'iyyar hamayya Svetlana Tikhanovskaya ta ba da shawarar cewa za ta iya tsayawa a matsayin shugabar riƙon ƙwarya.
Mutane da dama ne aka sa ran za su fara yajin aiki a Belarus, bayan da aka shafe karshen mako ana zanga-zangar neman shugaba Alexender Lukashenko ya sauka daga kan mulki.
An kiyasta cewa kusan mutane dubu dari ne suka mamaye babban birnin Minsk a ranar Lahadi, su na kira da a sake gudanar da zaben shugaban kasar da aka yi a makon jiya, kana shugaban ya sauka daga kan mukaminsa.
Jakadan Belarus a Slovakia, Igor Leshchenya, ya shaida wa BBC cewa sakamakon zaben da aka gudanar cike yake da rashin gaskiya, kana masu zanga-zangar na nuna cewa goyon bayan da shugaban ya samu a zahiri bai ma kai kashi 50 cikin 100 ba ballantana a yi tunanin cewa shi ne ya samu nasara.
Sakamakon zaben da hukumomi suka fitar dai ya bawa shugaban nasara da kashi tamanin bisa dari na kuri'un da aka kada.
Me ke faruwa a Belarus?

Asalin hoton, Reuters
Belarus ta samu kanta cikin zanga-zanga tsawon kwanaki, bayan gudanar da zaben da mutane da dama ke kyautata zaton cewa an tafka gagarumin magudi a cikinsa, wanda ya bawa shugaba Alexender Lukashenko nasarar ci gaba da zama a kan karagar mulkin kasar.
Bayan shafe mako guda ana tashin hankali da masu zanga-zangar adawa, an samu rahotannin cin zarafi da dama da ake zargin jami'an tsaron kasar sun aikata.
Shugaban kasar wanda ya shafe shekaru 26 a kan mulki, shi ne yafi kowanne shugaba dadewa yana jagoranci a nahiyar turai baki daya.
Shugaba Lukashenko na tafiyar da salon mulkinsa kamar na rushashshiyar tarayyar Soviet, in da ya mallaki yawancin kamfanonin gine-gine, sannan kafafoin watsa labaran kasar ma na mara masa baya.
Sannan ya jima yana bayyana kansa a matsayin mai tsatstsauran ra'ayin kishin kasa, in da ya ke nesanta kasarsa daga abinda ya kira ''Shishshigin kasashen waje''
Me kasashen duniya ke cewa ?

Asalin hoton, Reuters
Tarayyar turai da shugaban Faransa Emmanuel Macron sun ce za su ci gaba da marawa masu zanga-zanga baya don neman hakkinsu.
Wani karin mataki da tarayyar ta ce za ta dauka shi ne kakaba sabbin takunkumai ga kasar da ake kallon ta mayar da kanta saniyar ware a nahiyar.
To sai dai Russia, na goyon bayan shugaban ya ci gaba da kasancewa a kan mulki, ana ma sa ran shugaban Russia Vladmir Putin zai aike da jami'ai don tabbatar da gwamnatin Lukashenko ta ci gaba da wanzuwa.
Ita kuwa Amurka ta yi Allah wadai da zaben da ya gudana a makon da ya wuce, wanda ta bayyana a matsayin ''Zaben da ya tauye hakkin 'yan kasar''.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce kasar na duba yiwuwar kakabawa Belarus takunkumi, domin tilastawa shugabanninta soke zaben.











