Kuɗaɗen Abacha: Ireland za ta mayar wa Nigeria naira biliyan 2.5

Sani Abacha

Asalin hoton, others

Bayanan hoto, Transparency International ta ce Sani Abacha ya saci kusan naira tiriliyan biyu cikin shekara takwas da ya mulki Najeriya

Ƙasar Ireland ta ƙulla yarjejeniya da Najeriya domin mayar mata da dala miliyan 6.5 (naira biliyan biyu da rabi) da tsohon shugaban ƙasa Sani Abacha ya kwashe daga Najeriyar.

Ministan Shari'ar Najeriya, Abubakar Malami ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

Kuɗin na daga cikin kuɗaɗe na baya-bayan nan da Najeriya ke karɓowa daga cikin waɗanda ake alaƙantawa da waɗanda Sani Abacha ya kai ƙasashen waje daga ƙasar.

Sani Abacha ya mulki Najeriya daga shekarar 1993 zuwa 1998 kuma ƙungiyar Transparency International ta ce ya saci kusan dala biliyan biyar - fiye da naira tiriliyan biyu - jumilla a wannan tsakanin.

Ministar Shari'ar Ireland, Helen McEntee ta ce wannan ne karon farko da ƙasar za ta mayar wa Najeriya kuɗin.

"Mayar da kuɗin shi ne mataki irinsa na farko da Ireland ta ɗauka a matsayin wata hanyar tabbatar da jajircewarta wurin bai wa ƙasashen duniya haɗin kai domin yaƙar cin hanci," in ji ministar a cikin wata sanarwa.

Ireland ta toshe asusun ajiyar kuɗin a shekarar 2014 cikin wani ɓangare na aikin da ya kai ga toshe asusun kuɗaɗen da suka kai dala biliyan ɗaya a faɗin duniya, a cewar sanarwar.

Wannan na zuwa ne yayin da Najeriya ke faman neman kuɗin da za ta cike giɓin da ta samu a kasafin kuɗinta na 2020 sakamakon annobar korona.

A watan Mayu, Najeriya ta karɓi dala miliyan 300 na kuɗin Abacha daga Amurka da kuma yankin Jersey tare bayanan kafa kafa mata wasu sharuɗɗa.