Janar Sani Abacha

Muhimman abubuwan da suka faru a rayuwar marigayin
Shekara 20 kenan da mutuwar shugaban mulkin soja na Najeriya Sani Abacha

An zargi gwamnatinsa da yin kama-karya da take hakkin dan adam.

Har yanzu ra'ayoyin mutane sun bambanta a kan Abacha a Najeriya. Shugaba mai ci Muhammadu Buhari, wanda shi ma ya taba mulkin soja, ya yabe shi da cewa ya samar da ci gaba kamar gina tituna da bunkasa harkar ilimi da lafiya.

Ga dai wasu muhimman abubuwa dangane da rayuwar marigayin:

  • 20 ga watan Satumba1943
    WajeKano, Najeriya
    Kano, Najeriya hoto
    Bayani An haifi Janar Sani Abacha a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
  • 1963
    WajeKaduna, Najeriya
    Kaduna, Najeriya hoto
    Bayani Ya kammala makarantar horon aikin soji da ke Kaduna, ya kuma samu karin horo a Birtaniya.
  • 1965
    WajeNajeriya
    Najeriya hoto
    Bayani Ya auri Maryam Jiddah. Suna da 'ya'ya 10 tare, amma babban cikinsu ya mutu.
  • 1967-72
    WajeKudancin Najeriya
    Kudancin Najeriya hoto
    Bayani Abacha na daga cikin sojojin da suka yi yakin basasar Najeriya da aka yi da 'yan awaren Biafra, kuma ya ci gaba da samun girma a soja.
  • 1983
    WajeLegas, Najeriya
    Legas, Najeriya hoto
    Bayani Ya yi fice sosai a kasar saboda rawar da ya taka a juyin mulkin da aka yi wa gwamnatin Shugaba Shehu Shagari a ranar 31 ga watan Disamba. Bayan nan ne aka dora Janar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban mulkin soja.
  • 1985
    WajeLegas, Najeriya
    Legas, Najeriya hoto
    Bayani An hambarar da gwamnatin Janar Buhari da sa hannun Abacha. Ya kuma taimaka an dora Janar Ibrahim Babangida a mulkin kasar, shi kuma aka kara masa girma zuwa Manjo Janar.
  • 12 ga watan Yuni1993
    WajeLegas, Najeriya
    Legas, Najeriya hoto
    Bayani An gudanar da zabe don mika mulki ga farar hula kamar yadda aka dade ana jira. Kuma sakamakon farko-farko ya nuna cewa mashahurin mai kudin nan Moshood Abiola ke kan gaba, Janar Babangida ya soke sakamakon zaben.
  • Agusta1993
    WajeAbuja, Najeriya
    Abuja, Najeriya hoto
    Bayani An nada Abacha Ministan Tsaro, bayan da Babangida ya sauka ya kuma samar da gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin Ernest Shonekan.
  • 17 ga watan Nuwamba1993
    WajeAbuja, Najeriya
    Abuja, Najeriya hoto
    Bayani Shonekan ya yi murabus ya kuma mika mulki ga Abacha, a wani al'amari da mafi yawan mutane ke ganin kamar wani juyin mulkin ne. Ana ganin mulkinsa na cike da cin zarafin bil'adam da take 'yancin fadin albarkacin baki.
  • 1994
    WajeNajeriya
    Najeriya hoto
    Bayani Moshood Abiola ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa saboda cin zaben da 'ya 'yi' amma an kulle shi.
  • 1995
    WajeOgoni, Najeriya
    Ogoni, Najeriya hoto
    Bayani Mulkin Abacha ya fuskanci Allah-wadai daga kasashen duniya da dama kuma an dakatar da Najeriya daga kungiyar kasashe renon Ingila bayan da aka kashe masu kula da muhalli tara daga yankin Ogoni, wadanda suke zanga-zangar adawa da ayyukan gwamnati da kamfanin mai na Shell. Daga cikinsu akwai Ken Saro-Wiwa, wani mai rubuta wake, wanda kuma aka zaba cikin wadanda za a bai wa lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel.
  • 1996
    WajeAfirka Ta Yamma
    Afirka Ta Yamma hoto
    Bayani An zabi Abacha shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin kasashen Yankin Afirka Ta Yamma (Ecowas).
  • Fabrairu1998
    WajeSaliyo
    Saliyo hoto
    Bayani Abacha ya tura dakarun Najeriya zuwa Saliyo a wani kokari na hambarar da gwamnatin mulkin soja da kuma dawo da gwamnatin farar hula wacce aka hambarar shekara guda kafin nan.
  • 8 ga watan Yuni1998
    WajeAbuja, Najeriya
    Abuja, Najeriya hoto
    Bayani Abacha ya mutu sakamakon bugun zuciya da ake zargin shi ya yi sanadinsa, an kuma binne shi a wannan ranar. Shekara guda bayan nan ne Najeriya ta koma kan turbar dimukradiya.

Wadanda suka hada wannan aiki

Shiryawa: Yemisi Adegoke

Hadawa: Olawale Malomo

Tsarawa: Olaniyi Adebimpe

Hakkin mallakar hotuna: AFP, Getty Images, Ofishin Jakadancin Najeriya