Yaƙin Duniya II: Japan na bikin shekara 75 da gama yaƙin

Asalin hoton, EPA
Sarkin Japan Naruhito, ya bayyana "matuƙar takaici" game da abin da ƙasarsa ta aikata a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu yayin bikin cika shekara 75 da kawo ƙarshen yaƙin.
"Ina matuƙar fatan ba za a sake maimaita ayyukan yaƙi ba," a cewarsa a wurin bikin na ranar Asabar.
A gefe guda kuma, Firaminista Shinzo Abe ya yi alƙawarin "ba za a sake maimaita bala'in ba".
Firaministan ya ƙaddamar da bikin ne ta hanyar yin sadaka ga wata maƙabarta da ke ake ta ce-ce-ku-ce a kanta a birnin Tokyo, amma bai je da kansa ba.
Sai dai wasu ministoci huɗu sun ziyarci Maƙabartar Yasukuni a wani yunƙuri wanda ka iya ɓata ran ƙasashen China da Koriya ta Kudu.
Wannan ne karon farko cikin shekara huɗu da ake ganin babban ɗan siyasa ya ziyarci maƙabartar domin kai gaisuwa ga dakarun da aka ɗaure sakamakon laifukan yaƙi da kuma 'yan ƙasar da suka mutu sakamakon yaƙin.
"Na miƙa gaisuwa ne ga waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu a lokacin yaƙi," in ji Ministan Ilimi Koichi Hagiuda lokacin da yake magana da 'yan jarida.

Asalin hoton, Reuters
Sarki Naruhito mai shekara 60 ya yi taƙaitaccen jawabi a wurin taron, wanda aka ɗaga saboda annobar korona. Kusan mutum 500 ne suka halarta saɓanin 6,000 da suka halarta a shekarar da ta gabata.
Naruhito ya hau karagar mulki ne a watan Mayun bara bayan mahaifinsa Akihito ya zama sarki na farko da ya yi murabus a cikin fiye da shekara 200.











