Obadiah Mailafia: Kalaman tsohon mataimakin shugaban CBN kan Boko Haram sun bar baya da ƙura
Ku latsa hoton da ke sama don saurraon hirarsa da BBC Hausa.
Hukumar da ke sa ido kan kafafen yada labarai ta Najeriya ta ci tarar gidan rediyon Nigeria Info naira miliyan biyar, saboda zarginsa da yada kalaman ɓatanci bayan wata tattaunawa da ya yi da Dakta Obadiah Mailafia.
Dakta Mailafia, wanda tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya ne, ya yi zarge-zarge da dama a cikin tattaunawar, ciki kuwa har da zargin ɗaya daga cikin gwamonin arewacin Najeriya da jagorantar ƙungiyar Boko Haram.
Bayan wannan tattaunawa ta karaɗe shafukan sada zumunta ne hukumar tsaro ta farin kaya a ƙasar wato DSS ta gayyaci Dakta Mailafia a ranar Laraba domin gudanar da bincike kan irin zarge-zargen da ya yi.
Ko a ranar Laraban sai da ƙungiyar gwamnonin arewa suka yi kira da a zurfafa bincike kan irin zarge-zargen da Mailafia ya yi tare da kira ga duk wani ɗan Najeriya da ke da bayanai da za su taimaka wa jami'an tsaro wurin daƙile masu tayar da ƙayar baya da su fito su taimaka.
Sai dai ko bayan gayyatar da hukumar DSS ta yi wa Dakta Mailafia, BBC ta tattauna da shi ta waya inda ya ce ba a fahimci kalaman da ya yi ba, kuma bai ma san an naɗi kalaman nasa a bidiyo ba.
Obadiah ya ce a kasuwa ya tsinci zancen a bakin wasu Fulani.
A cewarsa, ya shaida wa hukumar DSS abin da ya sani kan wannan lamari kuma ba zai sake maimaita abin da ya faɗi ba, haka kuma ya nemi afuwa kan duk wasu bayanai da ya yi da suka ɓata wa wasu rai.
Ya kuma ce shi mai ƙaunar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne, "amma akwai mugayen mutanen da ba su ba shi shawarwarin da za su taimake shi".
Me gwamnatin Najeriya ta ce?
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Hukumar watsa labarai da al'adu ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter cewa hukumar da ke sa ido kan kafafen yaɗa labarai ta Najeriya ta ci tarar gidan rediyon Nigeria Info bisa laifin saɓa ƙa'idar aikin jarida.
Ta bayyana cewa gidan rediyon ya bai wa Dakta Mailafia dama domin faɗin wasu bayanai waɗanda bai tabbatar da su ba, kuma kalaman za su iya tayar da zaune tsaye, haka kuma an ci gidan rediyon tarar naira miliyan biyar domin hakan ya zama izina ga sauran kafafen watsa labarai, in ji hukumar.

Asalin hoton, FACEBOOK/Obadiah Mailafia
Me mutane ke cewa?
Jama'a da dama a shafukan sada zumunta na tafka muhawara da kuma bayyana ra'ayoyi daban-daban kan waɗannan kalamai da Mailafia ya yi, kuma kalaman da Mailafia ya yi da suka fi jan hankalin mutane su ne kan batun da ya ce akwai yiwuwar fara yaƙin basasa a shekarar 2022 da kuma kan batun akwai wani gwamnan arewa da ya ce kwamandan 'yan Boko Haram ne.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Barrister Bulama Bukarti, wanda mai sharhi ne kan tsaro ya bayyana cewa gayyatar da DSS suka yi wa Dakta Mailafia abu ne mai kyau kuma ya kamata bayan sun yi bincike, 'yan Najeriya su san wane ne gwamnan da ake zargi a matsayin kwamandan Boko Haram? Su wane ne kwamandojin da Mailafia yake tattaunawa da su? Kuma su wa za su fara yaƙin basasa a shekarar 2022?
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Zubairu Usman cewa ya yi yana da yaƙinin cewa wannan ba matalar addini ba ce, wannan ya fi kama da siyasa, suna yawan kawo addini domin ɗauke mana hankali su kuma su ci gaba da gudanar da sha'anin rayuwarsu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Wannan kuma cewa ya yi a ƙyale Mailafia, ya kuma ce shin ba a so a gano waɗanda suke ɗaukar nauyin Boko Haram? Ya bayyana cewa ya kamata ya tura bayanan da yake da su ga ofishin jakadancin Amurka kafin ya tafi wurin hukumar DSS ko da bai dawo ba.