Coronavirus: Shin cin 'ya'yan itace ko shan barasa na maganin cutar?

Wasu mata biyu sanye da takunkumin fuska suna magana da juna

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Daga Jack Goodman, Peter Mwai da kuma Flora Carmichael
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check

Yayin da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar korona a Afirka suka zarta miliyan guda a wannan makon, mun duba irin labaran karyar da ake yadawa a kan cutar.

An yada wani hoton bidiyo na shugaban kasar Ghana, amma kuma muryar da aka sanya a wannan bidiyon a kan cutar korona da aka danganta da shugaban kasar lallai ba shi ne ba ne.

Ba a san wanda ya yi magana da muryar ba, kuma magana ce irin ta 'yan Afirka, sai dai kuma ko shakka ba Nana Akufo-Addo ba ne.

Hoton shugaban kasar Ghana da kuma tutar kasar

Wasu bayanai ne da aka tattaro a kan karya da aka ce ya yi a game da cutar korona.

Kazalika an yi bayanan karya a kan batun samar da riga-kafin cutar korona da kuma yadda aka shigar da Bill Gates cikin batun.

A baya mun yi rubutu a kan batun rade-radin da ake yi a game da riga-kafin cutar korona.

Wani dan Najeriya da ya sanya wannan batun a shafin You Tube, sai da aka samu mutum fiye da dubu 400 da suka kalla.

Game da batun cewa shan barasa na magance cutar korona

Wannan batu ba gaskiya bane, amma kuma an yada shi a Afirka.

Wani hoton bidiyon wani mutum da ya mayar da martani a kan batun hana sayar da barasa a Afirka ta Kudu da aka nuna a wata tashar talbijin, ya samu dubban mutane da suka kalli wannan bidiyon.

An yi ta yada wannan bidiyon a kafofin sada zumunta da dama.

Wani hoton bidiyo

Wani mai barkwanci Thandokwakhe Mseleku, ya sanya wani bidiyon wata tattaunawa da aka yi dashi a talbijin a shafinsa na Instagram da kuma You Tube.

A cikin bidiyon yana cewa man da ake shafawa a hannu da ke kashe kwayoyin cuta na da sinadarin barasa kaso 70 cikin 100 a cikinsa, dan haka idan har mutum yana shan barasa to kamar yana kashe kwayoyin cutar da ke cikin jikinsa ne.

Wannan bayanai na sa ya sa da yawan mutane sun gasgata abin.

Game da batun cewa 'ya'yan itace ma na maganin cutar menene gaskiyar lamarin?

Wannan zance ba gaskiya ba ne, ana ta yada jita-jitar cewa amfanin da 'ya'yan itatuwa na maganin cutar a wasu kasashen Afirka, wannan ya sa da yawan mutane sun yarda da wannan batun.

Wani hoto da aka manna a wani asibiti a kan irin magunguna da abubuwan da ake ci a wuraren da ake killace masu cutar korona.

Wasu daga cikin abubuwan da aka sanya a cikin wannan takarda suna da matukar amfani a jikin dan adam.

Abin tambayar anan shi ne shin ko 'ya'yan itatuwa na kashe kwayar cutar korona?

'Ya'yan itatuwa akwai irin sinadaran da suke dauke da su da kuma amfanin da suke yi a jikin kowanne mutum.

Don haka batun wai ko 'ya'yan itatuwa na maganin cutar korona wannan ba gaskiya ba ne.

Wani gwajin riga-kafin cutar korona a Afirka ya haddasa mutuwar kananan yara biyu.

Wannan batu ba gaskiy bane.

.

Wani hoton bidiyo d aaka dauka a yayin wata tattaunawa a wani gidan talbijin da aka tattauna cewa ko wasu likitocin Faransa sun kshe wasu yara biyu a wajen gwajin ragakafin cutar korona

Wata mai rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta da ke zaune a Landan ya mayar da martani a kan batun likitocin Faransa, inda ta karyata cewa ba gaskiya bane likitocin sun yi sanadin mutuwar yara biyu wajen gwajin riga-kafin cutar korona.

Hoton bidiyon da aka yada wannan jita-jitar ya janyo ya mutsi a kan tituna.

A takaice dai an danganta wannan labarin ne da abin da ya faru tun tun a 2019 kafin ma bullar cutar korona.

Ma'aikatar lafiya ta Guinea a lokacin ta fitar da wata sanarwa inda tayi bayani a kan cewa wasu mutane sun mutu sakamakon yanayin da suka tsinci kansu bayan an basu maganin wata cuta.

A cewar sanarwar, babu wani da ya mutu saboda ya sha maganin cutar.

Karin labarai da za ku so ku karanta: