Coronavirus a Najeriya: Shin ƙasar na cin galaba a yaƙi da annobar?

Coronavirus a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mako guda kenan alƙaluman masu kamuwa da cutar a kullum yana raguwa
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja Bureau

Tun bayan da cutar korona ta ɓulla a Najeriya ranar 27 ga watan Fabarairun 2020 aka riƙa dasa ayar tambayar ko ƙasar za ta iya yaƙi da annobar kamar sauran ƙasashen duniya.

A faɗi a tashi, wata biyar kenan har yanzu waɗanda suka kamu da cutar ta korona a ƙasar ba su kai 50,000.

Idan aka kwatanta da wasu ƙasashe, za a iya cewa Najeriya ta sha duk da cewa annobar ba ta wuce ba, hasali ma ƙaruwa take yi a Brazil da Mexico da Amurka.

To ko hakan nasara ce da ƙasar ta yi a yaƙin ko kuwa dai kawai sa'a ce?

Adadi mafi girma na rana guda

Ranar Laraba 16 ga watan Yuni ne Najeriya ta ba da rahoton mutuwar mutum 31 sakamakon cutar ta korona, shi ne adadi mafi yawa na mace-macen da aka samu cikin sa'a 24 a ƙasar.

Sai kuma Laraba 1 ga watan Yuli, inda aka samu adadi mafi yawa zuwa yanzu na mutum 790 da suka kamu da cutar.

Adadin na raguwa

Kwana bakwai kenan a jere adadin masu kamuwa da cutar na raguwa a Najeriya, inda alƙaluman ranar Litinin suka nuna 288 ne suka kamu - rabon da a samu mutum ƙasa da 300 tun 7 ga watan Yuni.

  • 3 ga watan Agusta: 288
  • 2 ga watan Agusta: 304
  • 1 ga watan Agusta: 386
  • 31 ga watan Yuli: 462
  • 30 ga watan Yuli: 481
  • 29 ga watan Yuli: 404
  • 28 ga watan Yuli: 624

Yaya batun yin gwaji kuma?

Najeriya

Asalin hoton, NCDC

Bayanan hoto, Ya zuwa daren Talata mutum 289,133 aka yi wa gwajin korona a Najeriya

Najeriya mai mutum kusan miliyan 200 ta yi wa mutum 289,133 gwajin cutar korona ya zuwa daren ranar Talata.

Idan aka kwatanta da ƙasar Afirka ta Kudu sai a ce Najeriya ba ta yi ƙoƙari ba. Ya zuwa ranar Talata an yi wa mutum 3,058,695 a ƙasar mai mutum kusan miliyan 60.

Afirka ta Kudu na da mutum 516,862 da aka tabbatar sun kamu da cutar, sai 8,539 da suka mutu da kuma 358,037 da suka warke.

'Ana samu nasara a yaƙin da ake yi da cutar'

"Ni ina ganin duk da haka ana samun nasara a yaƙi da wannan cuta duk da cewa ba wai mun ƙarshenta ba ne," in Ji Farfesa Isa Abubakar na Jami'ar Bayero ta Kano.

Masanin kan cutuka masu yaɗuwa ya ƙara da cewa da ma a bayyane ta ke cewa Najeriya ba ta yin gwaji kamar sauran wasu ƙasashe.

"Amma duk da haka a cikin irin ɗan gwajin da muke yi ɗin aka samu wannan raguwar, sannan kuma su ma ɗakunan gwaje-gwajen ƙara yawansu ake yi ba raguwa suke ba. Yanzu muna da kusan 51 a ƙasa baki ɗaya."

Malamin jami'ar kuma mamba a kwamitin yaƙi da cutar a Jihar Kano, Farfesa Isa ya ce matakan da gwamnatocin jiha da na tarayya suke ɗauka su ma suna tasiri sosai.