Hate Speech: Abubuwan da ba ku sani ba kan dokar kalaman ƙiyayya a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ce daga yanzu duk mutumin da aka samu da laifin yin kalaman kiyayya zai biya tarar Naira miliyan biyar, wato kari sau dari kenan kan tarar da a baya aka sanya kan wannan laifi.
Ministan watsa labaran kasar Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja babban birnin kasar, lokacin da yake kaddamar da kwaskwarimar da aka yi wa dokar watsa labarai ta kasar.
Ya ce ya dauki matakin ne bayan samun amincewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya bukaci a sauya dokar sakamakon irin kalaman kiyayya da 'yan kasar suka rika yi a lokaci da kuma bayan babban zaben kasar na 2019.
A baya manyan jami'an gwamnati da ma mai dakin shugaban kasa Aisha Buhari sun koka kan yadda wasu 'yan kasar suke yada kalaman kiyayya da jita-jita suna masu yin kira a sanya ido kan yadda ake amfani da shafukan sada zumunta.
Hasalima a lokuta da dama jami'an tsaron kasar sun kama mutanen da ake zargi da yin kalamai na kiyayya, ciki har da mutumin da ya sanya wa karensa suna 'Buhari'.

Mene ne kalamin ƙiyayya?

Asalin hoton, Getty Images
Kalamin ƙiyayya ya ƙunshi furta wasu kalmomi ko wallafa wasu hotuna ko bidiyo da makamantansu da ka iya hasala wadanda aka yi dominsu.
Kazalika kalamin ƙiyayya ya hada da shirga ƙarya kan wani da kuma gauraya bayanansa da zummar muzanta shi ko ita.

Me sabuwar dokar ta ƙunsa?
Minista Lai Mohammed ya ce sabuwar dokar ta hukumar da ke kula da harkokin watsa labarai, wacce a turance aka kira Edition of the Broadcasting Code, ta yi garambawul kan yadda ake watsa labaran siyasa, labarai na cikin gida, labaran da ke faruwa kai-tsaye, tallace-tallace da kuma yaki da halayyar goyayya tsakanin kafafe watsa labarai.
- Dokar ta kara adadin tarar da mutumin da aka samu da laifin kalaman kiyayya zai biya daga N500,000 zuwa N5m.
- Dokar yin rijista ga shafukan intanet ta bai wa Najeriya damar sanya ido kan kafafen watsa labarai na kasashen waje domin ganin ba su watsa labaran da za su yi wa kasar illa ba.
- Dokar ta ce alhakin kafafen watsa labarai ne su samar da lokacin bayar da labarai a lokacin da kasar ta fada cikin masifu.
Masana harkokin watsa labarai da wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu kan batun.
Tsohon shugaban hukumar kula da kafafen watsa labaran kasar Tony Iredia ya caccaki Mr Lai Mohammed kan wannan sabuwar doka, yana mai cewa ta keta tsarin watsa labarai.
Sai dai wani da ke amfani da shafin Twitter, Justin, ya ce bai ga wata matsala kan dokar ba idan har gwamnati za ta iya bambancewa tsakanin kalaman kiyayya da kuma kalaman fadin albarkacin baki
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Sai dai ministan ya ce: "Ba mu damu da [masu sukar wannan doka] ba saboda muna yi ne domin ci gaban kasarmu. Kundin dokar kafafen watsa labaran ba abu ne da ba zai sauya ba. Abu ne da za a iya sake nazari akansa lokaci zuwa lokaci."











