Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Rashin wurin wanke hannu ne silar wasu cutuka da ake ɗauka a asibitocin Najeriya'
Kwamitin shugaban ƙasa kan yaƙi da cutar korona a Najeriya ya ce ya samar da wuraren wanke hannu da dama a manyan asibitocin tarayya a ƙoƙarinsu na kare bazuwar cutuka a cibiyoyin kula da lafiyar.
Babban jami'in kwamitin, Dakta Sani Aliyu ya ce cutuka da yawa da ake ɗauka a asibitocin Najeriya, na da alaƙa da rashin wuraren wanke hannu.
"Rashin ruwan wanke hannu, shi kansa matsala ne. Ba ma a lokacin (da ake fama da annobar) kobid ba. A'a har sauran lokuta a baya," in ji babban jami'in lafiyar na Najeriya.
Ya ce hakan ta sa, sun samar da manyan baho-baho inda ma'aikatan lafiya za su riƙa zuwa don wanke hannuwansu.
Jami'in ya kuma ce akwai ma'aikatan lafiya a Najeriya sama da 1,000 da aka tabbatar sun kamu da cutar korona ya zuwa wannan lokaci.
A wannan makon ne Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa, fiye da ma'aikatan lafiya dubu goma ne suka kamu da cutar Korona a yankin Afirka, kudu da hamadar sahara tun daga farkon bullar annobar.
Adadin dai ya kai kimanin kashi 10 cikin dari na ma'aikatan lafiyar da suka kamu da cutar a fadin duniya, duk da yake, masu cutar a Afirka ba su da yawa idan an kwatanta da sauran sassan duniya.
Dakta Sani Aliyu ya ce duk mutum ɗaya cikin waɗanda suka kamu da cutar korona ashirin a Najeriya ma'aikatan lafiya ne.
Ya ce hakan ta faru ne saboda yanayin aikin ma'aikatan lafiya waɗanda alhakinsu ne yin mu'amala da kuma tallafawa mutanen da suka kamu da cutuka ko kuma suke fama da jinya.
Babban jami'in lafiyar ya ce gwamnatin Najeriya ta yi ƙoƙarin ɗaukar matakai don kare ma'aikatan lafiyan ƙasar daga kamuwa da cutar ta korona.
A cewarsa, gwamnati ta tabbatar da samar da tufafin kare ma'aikatan lafiya da ake kira da PPE a Ingilishi, tare da samar da horo kan yadda ake amfani da tufafi.
Dakta Sani Aliyu ya ce ƙoƙarinsu ya kai ga horas da ma'aikatan lafiya kimanin 18,000 kan hanyoyin kare kai daga kamuwa da annobar korona.
Zuwa yanzu dai, akwai mutum kusan 40,000 da suka kamu da cutar a Najeriya, wasu fiye da 800 ne aka tabbatar da mutuwarsu sanadin cutar a ƙasar.