Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saudiyya za ta hana zuwa filin Arafat da Muzdalifah sai da izini
Ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa daga ranar Lahadi, za a saka dokar hana shiga wasu wuraren ibada na ƙasar sai da izini.
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa an ɗauki wannan matakin ne sakamakon shirin da ƙasar ta ke yi na gudanar da Aikin Hajji da mutane ƙalilan.
Jami'an tsaro a ƙasar za su hana shiga Mina da Muzdalifah da kuma Arafat sai da izini.
An bayyana cewa duk wanda ya karya wannan doka, zai biya tara da ta kai ta riyal 10,000, kimanin kuɗin Najeriya sama da naira miliyan ɗaya kenan.
Jami'an kuma za su ci gaba da sintiri kan duka hanyoyin da ke kai wa zuwa wuraren ibadar domin tabbatar da an bi dokar da kuma yin tara ga waɗanda suka karya dokar.
A kwanakin baya ne dai ƙasar ta sanar da cewa kashi 70 cikin 100 na waɗanda za su gudanar da Aikin Hajji na bana baƙi ne mazauna Saudiyya sai kuma sauran kashi 30 ɗin ne asalin 'yan ƙasar.
Ƙasar ta ce adadin waɗanda za su gudanar da Aikin Hajjin ba za su wuce mutum 10,000 ba sakamakon daƙile yaɗuwar cutar korona.
Mutum 248, 416 ne suka kamu da cutar korona a Saudiyya, inda kuma mutum 2,447 suka mutu tun bayan ɓullar cutar a ƙasar.