Boko Haram: 'Za mu ɗauki mataki kan harin jirgin Majalisar Ɗinkin Duniya'

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da harin da 'yan Boko Haram suka kai wa jirgi mai saukar ungulu na Majalisar Ɗinkin Duniya.

A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasar ya fitar kan harkokin watsa labarai Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce "za mu ɗauki mataki kan harin da aka kai da ya yi sanadiyar mutuwar mutum biyu har da jinjiri ɗan shekara biyar".

Sanarwar ta shugaban ƙasar na zuwa ne bayan Majalisar Ɗinkin Duniyar ta yi kira ga gwamnatin ƙasar ta gudanar bincike kan harin tare da gaggauta hukunta waɗanda suka aikata laifin.

Shugaban ya kuma yi kira ga ma'aikatan bayar da agaji da ke aiki a yankin arewa maso gabas ta a kowane lokaci sun rinƙa shirya tafiye-tafiyen su - ta jirgi ko mota tare da haɗin kan jami'an tsaro.

Tun a ranar Asabar ne dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah wadai da wannan hari da ƙungiyar Boko Haram ta kai kan ɗaya daga cikin jiragenta masu saukar ungulu a yankin Damasak na jihar Borno a arewa maso ƙasar.

Lamarin ya faru ne ranar 2 ga watan Yuli kuma ko da yake babu abin da ya faru da ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniyar, amma ya yi sanadin mutuwar mutum biyu, ciki har da yaro ɗan shekara biyar, a garin na Damasak.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Asabar, shugaban sashin jinƙai na hukumar da ke Najeriya Edward Kallon ya bayyana cewa harsasai da 'yan tayar da ƙayar bayan suka harba wa jirgin ya lalata shi kuma ya tsayar da ayyukan jinƙai da ake yi a yankin na arewa maso gabas.

"Ina Allah wadai da duk wani hari kan farar hula da kayayyakin aikin jinƙai da ma'aikatan agaji, kuma ina kira ga duk jami'an tsaro da ke riƙe da makamai da su girmama dokokin haƙƙin bil adama na ƙasa da ƙasa su kuma tabbatar da kare farar hula da ma'aikata da kayayyakin aikin jin ƙai," in ji Mista Edward.

Ya kara da cewa: "Ina mika ta'aziyya ga iyalan fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba wadanda harin ya rutsa da su kuma ina addu'ar samun sauki ga wadanda suka jikkata sanadin hari."

Ko a cikin watan Yuni na wannan shekara sai da 'yan Boko Haram ɗin suka kai hari garin Monguno, matattarar ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙasashen waje.

A harin na Monguno, an tabbatar da kashe a ƙalla sojoji 20 da farar hula sama da 40.

Ko a shekarar 2011, sai da wata mota ɗauke da bam ta kai hari a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja, inda ta yi sanadiyar mutuwar mutum 18.

Tashin bam din dai ya lallata hawa daya na ofishin, inda bam din ya jikkata a ƙalla mutane sittin.