NDDC: 'Abin da muka gano a badaƙalar Hukumar Naija Delta'

Prof. Daniel Kemebradikumo Pondei na hukumar NDDC

Asalin hoton, FACEBOOK / NDDC

Bayanan hoto, Farfesa Daniel Kemebradikumo Pondei na hukumar NDDC
Lokacin karatu: Minti 4

Zaman kwamitin majalisar wakilan Najeriya ya yi ranar Litinin a Abuja ya haifar da wasu abubuwan da suka ja hankulan ƴan Najeriya, musamman ma yadda shugaban hukumar raya yankin Naija Delta, NDDC Farfesa Daniel Pondei ya riƙa suma yayin da yake amsa tambayoyi daga ƴan majalisar.

Amma akwai batutuwan da abin da ya auku a zaman kwamitin ya kusa binnewa - kamar ainihin dalilan da suka sa majalisar ke bincikar hukumar ta NDDC da abubuwan da ta gano kawo yanzu.

An kuma jima ana kai ruwa rana tsakanin ƴan kwamitin da kuma Godswill Akpabio wanda shi ne ministan da ke kula da ma'aikatar raya yankin Naija Delta.

Kabiru Alhasan Rurum na cikin ƴan kwamitin, kuma ya yi wa BBC bayani kan abin da bincikensu ya gano.

Cikin abubuwan da kwamitin ya gano, akwai "bayanai da muka samu daga ofishin babban akawu na ƙasa da kuma babban bankin Najeriya waɗanda dukkansu sun kawo bayanai a rubuce na yadda suka saki kuɗade ga wannan ɓangare".

Ya kuma bayyana cewa bayanan sun sanar da kwamitin yadda hukumar NDDC ta salawantar da maƙudan kudaden da aka ware domin ayyukan raya yankin na Naija Delta:

"A bayanan da shugabannin hukumar suka gabatar gaban kwamitin majalisa, sun kama kansu, na farko dai sun ce sun kashe Naira biliyan 81.5 - kuma kowa ya san halin da ake ciki a ƙasar nan da ma sauran duniya. Babu wata ma'aikata da ta gudanar da wasu ayyuka na a-zo-a-gani."

Ya ce tabbas ƴan Najeriya za suyi mamaki su ji cewa an kashe irin waɗannan kuɗaɗe.

Wannan layi ne

Kalli yadda shugaban hukumar NDDC Farfesa Daniel Pondei 'ya rika suma' yayin zaman kwamitin da ke binciken hukumar da yake jagoranta:

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

A kan batun halin da shugaban riko na hukumar ta NDDC ya shiga mai kama da suma, ɗan majalisa Rurum ya ce an wa shugaban NDDCn tambayoyi fiye da goma gabanin ya fara suma.

"An yi masa tambayoyi kamar 11, kuma bai iya amsa ko da ɗaya ba cikinsu, kuma shi yasa mu kayi wannan zaman kai tsaye har muka kira gidajen talabijin sun nuna wannan zama namu na wajen sa'a shida," inji ɗan majalisar.

Ya kuma ce wasu da ke cikin ɗakin taron na ganin ciwon da shugaban NDDCn ya ce ya kama shi na gaske ne, amma wasunsu na ganin shiri ne kawai domin ya kauce amsa tambayoyin da ake ma sa.

Bayan da aka fice da shugaban hukumar domin a duba lafiyarsa, shugaban majalisar ya sanar cewa ba za neme shi ya dawo ya ci gaba da amasa tambayoyin ƴan kwamitin ba.

Ɗan majalisa Rurum ya ce wannan bai zama matsala ba, domin gabanin matsalar da ta faru, sun karbi bayanai a rubuce daga bangaren hukumar.

Wannan layi ne

Bahasin Ministan Neja Delta Godswill Akpabio

Sanata Godswill Akpabio, ministan yankin Neja Delta na Najeriya

Asalin hoton, Twitter/Akpabio

Bayanan hoto, Sanata Godswill Akpabio, ministan yankin Neja Delta na Najeriya

Bayan ficewar shugaba hukumar, kwamitin ya kira Sanata Godswill Akpabio, ministan ma'aikatar Neja Delta

Sanata Godswill Akpabio ya musanta wasu daga cikin zarge-zargen da tsohuwar shugabar hukumar ta NDDC mai suna Joy Nunieh tayi ma sa, misali wanda aka ce ya riƙa kwace ayyukan hukumar da kuma cewa ya kori wasu ma'aikatan hukumar.

Ga wasu abubuwan da ya gaya wa kwamitin binciken:

  • Ya ce ba aikin ministan Neja Delta ne ya rika tafiyar da ayyukan yau da kullum na hukumar ta NDDC ba.
  • Ya sanar cewa ba shi da sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙasar.
  • Ya musanta zargin da aka yi ma sa cewa ya nemi wani ma'aikacin hukumar ya ba shi naira biliyan 10.
  • Bai taba karbar ko kwabo ba daga hukumar NDDC tun da ya zama minista, kuma bai taba yin kwangila a can ba.
  • Ya ce babu ƙanshin gaskiya da ak ce wai wasu naira biliyan 40 sun ɓace a asusun hukumar saboda suna bin tsarin gwamantin Najeriya na zuba dukkan kuɗaɗensu a asusu ɗaya ne.
  • Ya ce tsohuwar shugabar riƙo ta NDDC ta kashe naira biliyan 23 ne, ba naira bilyan takwas ba.
Wannan layi ne

In ba ka iya kama ɓarawo ba...

Shi ma bahasin da ministan ya bayar a gaban kwamitin ya kasance cike da taƙardama, inda aka riƙa kai-komo tsakaninsa da ƴan kwamitin.

Ɗaya daga cikin batutuwan da suka ja hankalin mutane yayin bahasin da yake bayar wa shi ne na yadda aka kashe maƙudan kudaden hukumar a ƙarƙashin kulawarsa.

Akpabio ya ce kashi 60 cikin 100 na kwangilolin da hukumar NDDC ta bayar, ƴan majalisar ƙasa ne suka amfana da su. Wadannan kalaman nasa sun janyo cece kuce tsakaninsa da daya daga cikin mabobin kwamitin bayan da ya tamabaye shi abin da majalisar ƙasa ta taɓa ƙaruw ada shi daga hukumar ta NDDC.

Kwamitin ya binciki shugaban hukumar Farfesa Daniel Pondei da ministan ma'aikatar ta Neja Delta Godswill Obot Akpabio kan tuhumar da ke yi wa shugabannin riƙo na hukumar na karkatar da daruruwan miliyoyin naira da aka ware domin raya yankin Neja Delta da ya daɗe yana fama da gurbacewar yanayi saboda ayyukan haƙo man fetur a yankin.

Kabiru Alhasan Rurum ɗan kwamitin majalisar da ke binciken hukumar ta NDDC ya bayyana mataki na gaba da majalisar za ta ɗauka ganin cewa an kammala ƙarbar bahasin:

"Yanzu za mu rubuta rahotonmu, kuma za mu gabatar da shi a gaban majalisar ƙasa inda za a tafka mahawara gabanin miƙa abin da muka gano ga ofishin shugaban ƙasa domin ya ɗauki matakin da ya dace."