Yadda Amurka ta kama fitattun 'yan Najeriya na Instagram da dala miliyan 40

mrwoodbery in front of Lamborghini

Asalin hoton, mrwoodbery

    • Marubuci, Daga Larry Madowo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Dan jarida mazaunin Amurka
  • Lokacin karatu: Minti 4

Kwana ɗaya bayan cika shekaru 29 da haihuwarsa a watan Mayu, Olalekan Jacob Ponle ya wallafa hotonsa a shafin Instagram inda yake tsaye kusa da wata mota ƙirar Lamborghini a Dubai.

"Ku bar bari mutane na sa ku kuna jin ba ku yarda da kanku ba dangane da dukiyar da kuka mallaka," ya yi gargaɗi kan saka kayayyaki masu tsada da kuma sauran kaya samfurin Gucci daga sama har ƙasa.

Bayan wata ɗaya, an kama ɗan Najeriyar nan mai suna "mrwoodberry" na Instagram a Dubai, inda 'yan sanda suka kama shi da zargin almubazaranci da kuɗi da kuma damfara.

Cikin gwamman 'yan nahiyar Afrika da 'yan sandan suka kama akwai wani wanda mai shekaru 37 wanda ya yi fice a cikinsu mai suna Ramon Oloruna Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Hushpuppi ko kuma hush na da mabiya miliyan 2.4 a Instagram.

'Yan sanda a ƙasar sun bayyana cewa sun gano dala miliyan 40 lakadan a gidansa tare da motocin alfarma 13 da kuɗinsu ya kai dala miliyan 6.8 da kuma kwamfutoci 21 da wayoyin hannu 47 da kuma adireshin kusan mutum miliyan biyu da ake zargin ya damfara.

Kauce wa Instagram, 1
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram, 1

Presentational white space

Tuni aka tafi da Mista Abbas da kuma Mista Ponle zuwa ƙasar Amurka inda ake tuhumarsu a wata kotu a Chicago da zargin damfara ta intanet da kuma halarta kuɗin haram na miliyoyin daloli.

Har yanzu ba a nemi waɗanda ake zargin da su ɗaukaka ƙara ba sakamakon ba a yanke hukunci aka gano ko suna da gaskiya ko ba su da ita ba.

"Ina tunanin akwai nau'i na fankama a tattare da su sakamakon suna tunanin suna takatsan-tsan da yadda suke aikinsu a intanet, amma suna rayuwa ta ƙasaita tare da nuna kawunansu a kafafen sada zumunta," in ji Glen Donath, wani tsohon mai shigar da ƙara da ke ofishin lauyoyin ƙasar Amurka.

Yadda suka rinƙa nuna kansu a kafafen sada zumunta ne ya sa aka fara saka alamar tambaya kan yadda suke samun kuɗi.

Da kansu suka bayar da bayanai a kansu ga masu bincike na ƙasar Amurka sakamakon yadda suke wallafa abubuwan da suke yi a Instagram Snapchat.

A shafin Instagram, hushpuppi ya fake da cewa shi mai harkar gidaje ne kuma yana da rukuni na bidiyoyi a shafinsa da ya saka wa "Flexing".

Hari ga wani kulob na Turai

A watan Afrilu, Hushpuppi ya sake biyan kuɗin hayarsa a rukunin gidaje na Exclusive Versace Apartments da ke Dubai ƙarƙashin sunansa da kuma lambar wayarsa.

"Ina godiya ga ubangiji dangane da albarkar da ka saka a rayuwata. Ina kira gare shi ya kunyata waɗanda suke jira na kunyata," ya saka hoton wata mota ƙirar Rolls-Royce kwanaki kaɗan kafin a kama shi.

"Abbas na samun waɗannan kuɗaɗen ne ta hanyar aikata laifuka, kuma yana daga cikin shugabannin ƙungiyoyin masu damfara ta intanet da kuma halarta kuɗin haram, inda suke damfarar mutane a faɗin duniya," in ji ƙungiyar bincike da FBI a Amurka.

Kauce wa Instagram, 2
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram, 2

Presentational grey line

A wani lamari da ya faru, wani kamfanin ya yi zargin cewa ya rasa kuɗaɗe da suka kai dala miliyan 14.7 ta hanyar damfara ta intanet inda kuɗin kuma suka ƙre a asusun ajiya na hushpuppi a ƙasashe a dama.

A takardar koken, an yi zargin cewa yana ɗaya daga cikin wani shiri da aka yi na satar dala miliyan 124 daga wani kulob na ƙwallo na nahiyar Turai.

FBI ta samu bayanai daga Google dinsa da Apple iCloud da Instagram da Snapchat waɗanda ake zargin cewa suna ɗauke da bayanai na banki da fasfo dinsa da kuma tattaunawarsa da waɗanda ake zargi da yunƙurin aikata laifin.

Wani bincike da wani kamfanin samar da tsaro na Agari ya yi ya gano cewa kusan kashi 90 cikin 100 na damfara da ake yi ta hanyar email na zuwa ne daga Afrika ta Yamma.

'Yan damfara ta intanet'

Koken da aka kai kan Mista Abbas da kuma Mista Ponle ya nuna a zahiri abubuwan da suke yi ya yi kama da abin da kamfanin tsaron yake kira "Vendor Email Compromise Tactics," wanda hakan wata dabara ce da 'yan damfara ke shiga adreshin email din mutum su yi abin da suka ga dama.

Ta hakan, suna lura da da kuma sa ido kan maganganu da ake yi tsakanin mai siya da siyarwa.

Larry Madowo
Larry Madowo
The 'Nigerian prince' trope has become shorthand for deception"
Larry Madowo
Journalist
Presentational grey line

"Masu damfarar za su tattara bayanai su jira har lokacin da saƙon email din zai iso," in ji Crane Hassold, wani babban darakta a kamfanin tsaro na Agari.

"Ɗan damfarar zai juya saƙon email ɗin zuwa nasa, ya rubuta sabon saƙon email ga kwastoma ɗin wanda zai yi kama da ya zo daga mai sayarwa, wanda sabon email din zai alamta cewa mai sayarwan ya samu matsala da asusun ajiyarsa, sai su bayar da sabon asusun ajiya, daga nan sai kuɗin su tafi."

Mista Ponle wanda aka fi sani da "mrwodberr," na amfani da Mark Kain a email dinbsa, in ji FBI.

Ana zarginsa da damfarar wani kamfani a Chicago dala miliyan 15,2. Akwai wasu kamfanoni a Iowa da Kansas da Michigan da New York da California da ake zargin ya damfare su.

Damfara a intanet ta zama ruwan dare a duniya inda kuma ana yawan alaƙanta hakan da Najeriya.

Masu irin wannan aika-aika a ƙasar na da laƙabi inda ake kiransu da Yahoo boys.

Presentational grey line