Hushpuppi: Me ya sa APC, PDP da Atiku ke ce-ce-ku-ce kan 'ɗan damfara'?

Photo of Atiku, Saraki and Melaye

Asalin hoton, TWITTER/ATIKU/SARAKI/DINO

Lokacin karatu: Minti 2

Jami'iyya mai mulki a Najeriya ta APC ta buƙaci hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC da kuma hukumar leƙen asiri kan hada-hadar kuɗi wato NFIU su bincike wasu manyan 'yan jam'iyyar PDP.

APC ta yi wannan kiran ne bayan hoton wasu jiga-jigan 'yan jam'iyyar ya karaɗe shafukan sada zumunta inda aka gansu tare da Ramoni Igbalode wanda aka fi sani da Hushpuppi.

A 'yan kwanakin nan ne dai aka kama Hushpuppi a Dubai bisa zargin damfara da almundahanar maƙudan kuɗaɗe.

Jam'iyyar APC a Najeriya ta ce ya kamata a binciki Atiku Abubakar da kuma Bukola Saraki da kuma tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara da kuma tsohon Sanata wato Dino Melaye bisa alakarsu da Hushpuppi.

..

Asalin hoton, Instagram/hushpuppi

Sai dai mai magana da yawun jam'iyyar PDP Kola Ologbodian ya shaida wa BBC cewa har yanzu jam'iyyarsu ba ta zauna ta tattauna kan wannan zargin da ake yi musu ba.

APC ta bayyana cewa manyan 'yan jam'iyyar ta PDP sun ɗauki hotuna da Hushpuppi a gidansa a lokacin da suka ziyarci Dubai, a wata sanarwa da mataimakin sakataren watsa labarai na jam'iyyar Yekini Nabena ya fitar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

A martanin da ya mayar, mai bai wa Atiku shawara kan harkokin watsa labarai Justice Paul Ibe, ya ce abin mamaki ne a ce APC ta zargi Atiku na da alaƙa da Hushpuppi don kawai sun ga sun yi hoto tare a wurin wani biki.

Shi ma Bukola Saraki ya ce: "Sanarwar APC, jam'iyyar da ke mulki a kasarmu, na daya daga cikin hanyoyin da aka kassara hukumomin yaki da cin hanci kuma shi ne dalilin da ya sa kasashen duniya suke kokwanto kan gaskiyar yaki da cin hancin da hukomin suke yi.

"Abin da ya sa kuwa shi ne, wadannan mutane da ake zargi da zamba a shafukan intanet sun fitowa fili suna nuna irin arzikinsu, kuma APC ba ta ga wani abin kyama game da hakan ba. Kazakila, jam'iyyar ba ta ga dacewar kiran hukumomin da ke yaki da cin hanci domin su yi bincike kan lamuransu ba."

Kwanaki kaɗan dai bayan kama Hushpuppi, an tafi da shi Amurka inda hukuamr FBI a ƙasar ta maka shi kotu kan zarge-zarge da dama masu alaƙa da damfara ta intanet.

Sun kuma zarge shi da sata a wani kamfani na Amurka da kuma wani banki na daban, idan aka kama shi da wannan laifi, akwai yiwuwar zai shafe a kalla shekaru 20 a gidan yari.