Coronavirus a Najeriya: Abin da ya sa aka ɗage dawo da jigilar jiragen sama

Arik air

Asalin hoton, Image copyrightBOEING HANDOUT

Kamfanonin jiragen sama a Najeriya sun ce akwai yiwuwar ba za su fara jigila ba, har sai bayan sun warware wasu matsaloli da suka dabaibaye sabon tsarin.

Wannan kuwa ya taso ne bayan da umarnin da gwamnati ta bayar ya nuna a fara zirga-zirga a ranar 21 ga watan Yuni.

Za dai a ce ta leko ta koma sakamakon wasu rahotanni da ke yawo kuma ake dangantasu da kwamitin yaki da cutar coronavirus a kasar cewa babu tabbacin ranar bude harkokin sufuri na jiragen sama na cikin gida, wani abu da ya yi karo da wasu rahotanni tun farko da suka nuna cewa za a fara zirga-zirgar daukar fasinjoji daga ranar 21 ga wannan wata.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kwamitin yaki da cutar COVID-19 ya nuna ba zai yiwu a fara jigilar fasinjoji ta jiragen sama a ranar 21 ga wannan wata ba.

Tun farko an nuna kwamitin ya bukaci kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama da su je su yi nazari kan fara zirga-zirga da kuma dawo mata da amsa a ranar 21 ga watan Yuni.

Amma kamfanonin suka yi wa wannan umarni gurguwar fahimta.

Captain Ado Sanusi shi ne manajan daraktan kamfanin jiragen sama na Aero contractors da ke Najeriya.

Wasu daga kamfanonin jiragen saman dai sun cika shafukansu na sada zumunta da yanar gizo da sabon farashin kudin kowacce kujerar fasinja, kusan wanda ya ninka tsohon farashi kafin bayyanar cutar korona.

Wannan dai na nuna cewa fasinjojin da suka sayi tikitin jirgin sama da niyyar fara tafiya cikin biranen kasar daga ranar 21 ga watan Yuni, za su jira har sai bayan samun cikakkun bayanai daga ma'aikatar sufuri a kasar.

Fasinjoji da dama sun bayyana rashin jin dadinsu kan wannan lamari.

Bayanai sun nuna gwamnatin tarayya ba ta kammala gamsuwa da tsarin jiragen sama don fara aiki ba, bisa la'akari da cewa sun shafe kimanin wata biyu ba tare tashi ko sauka ba. Ma'ana jiragen na suna bukatar a yi musu gyara da duba lafiyarsu kafin su fara daukar fasinjoji.

To sai dai kamfanonin na cewa sun shirya tsaf, tun bayan samun sanarwar cewa za su koma bakin aiki a ranar 21 ga watan na Yunin bana.