Coronavirus a Saudiyya: An dauki matakan hana cunkoso a Masallacin Ka'aba

Asalin hoton, Harmain
Hukumar da ke kula da Masallatai Biyu Masu Tsarki na Makkah da Madina wato Haramain ta fitar da sabbin matakai da aka dauka don rage cunkoso idan aka dawo da yin Umara da Dawafi nan gaba, a kokarinta na rage sake yaduwar cutar korona.
Hukumar Haramain ta fitar da wannan sanarwa ne a shafinta na Twitter a ranar Talata, sai dai ta ce sanarwar ba ta nuni da ranar da za a bude masallacin ga masu Umara da masu Dawafi.
Ta ce an fitar da wadannan matakai ne bayan da kwamitin kwararru na masallacin ya yi bincike kan yadda abubuwa za su kasance a lokacin da aka bude masallacin don yin Umara da Dawafi.
Matakan sun hada da:
1. Za a dinga amfani da Kofar Sarki Fahad don shiga harabar Dakin Ka'aba don a samu sarari sosai da kuma Kofar Jisr Annabi da Kofar Safa don masu ibada su samu damar fita daga harabar Ka'aba ta hanyar bin matakalar bene.
2. Za a ware kofofi masu lamba daga 89 zuwa 94 don shiga harabar da ake Dawafi ta kasa da kuma fita ta Kofar Ajyad
3. Za a dinga amfani da Gadar Ajyad da ke kudancin masallacin da Gadar Shabeika da ke yamma don shiga harbar da ake dawafi ta kasa. Su kuwa matakalar bene masu amfani da inji da Gadar Safa za su zama wajen fita
4. Za a samar da hanyoyi da dama da mutane za su dinga bi don shiga harabar Ka'aba don tabbatar da cewa an bi dokokin yin nesa-nesa da juna tsakanin masu ibada
5. Za a dinga amfani da sabon bangaren Sarki Fahad da Sarki Abdullah don samun isasshen waje ga masu sallah

Asalin hoton, Haramain
6. Za a dinga dawafi a harabar dakin ka'aba da kasa, amma za a bar hawa na farko ga tsofaffi da marasa karfi don yin dawafi
7. Za a sanya shinge uku a wajen yin dawafi don raba tsakanin masu dawafi a kokarin bin dokar yin nesa-nesa da juna
8. Za a rufe duk wata hanya ta shiga garin Makkah da sassafe musamman a ranar Juma'a
9. Za a bukaci otel-otel da ke kusa da Harami su dinga kayyade yawan bakinsu da za su shiga cikin masallacin sallah, za a so su dinga shawartar bakin da su dinga bin sallar daga masaukinsu
10. Za a kirkiri wata manhaja mai suna Tawakkalna da za a dora a wayoyin komai da ruwanka wacce mutane za su dinga neman izinin shiga masallacin a kanta
11. Za a sanya shingayen bincike a kan hanyar zuwa Harami da kuma harabarsa
12. Za a hana shiga garin Makkah daga karfe 9 na safe har zuwa 8 na dare ga duk wadanda ba mazauna birnin ba da kuma wadanda ba su da izinin shiga.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X











