Chelsea tana son dauko Werner, Messi yana nan daram a Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea tana duba yiwuwar mayar da hankali wajen dauko dan wasan RB Leipzig Timo Werner, mai shekara 24, idan dan kasar ta Jamus ya bayyana sha'awar komawa can. (ESPN)
Shahararren dan wasan da ya lashe kyautar Ballon d'Or sau shida Lionel Messi, mai shekara 32, zai ci gaba da zama a Barcelona zuwa kakar wasa ta badi bayan wa'adin damar da aka ba shi ta barin kungiyar don radin kansa ya wuce. (Standard)
Real Madrid ta yi watsi da damar karbo aron dan wasan Chelsea Willian, mai shekara 31. Kwangilar dan wasan na Brazil za ta kare a Stamford Bridge a bazara. (Mirror)
Manchester United za ta biya £10.5m saboda tsawaita zaman aron dan wasan Najeriya mai shekara 30, Odion Ighalo, zuwa watan Janairu - za a bai wa Shanghai Shenhua £6m sannan £130,000 su zama alawus-alawus na duk mako. (Mail)
Liverpool tana tattaunawa da zummar tsawaita zaman aron dan wasan Wales mai shekara 23, Harry Wilson a Bournemouth da kuma dan wasan Ingila Rhian Brewster, mai shekara 20, a Swansea zuwa karshen kakar wasa ta bana. (Telegraph)
Arsenal ta shirya domin sabunta kwangilar dan wasan Brazil David Luiz, mai shekara 33, zuwa shekara daya amma za ta rage alawus dinsa na na mako-mako £130,000. (Mirror)
Kocin Ingila Gareth Southgate ba zai halarci wasannin Gasar Premier ba idan aka koma fagen daga saboda yana ganin halartarsa ba ta da amfani. (Star)
Kungiyoyin Gasar Premier za su tattauna ranar Alhamis kan yiwuwar barin koci-koci da mataimakansu su rika hira da gidajen talbijin yayin hutun rabin lokacin wasanni. (Express)
Chelsea ta mika wata bukata ga hukumar Gasar Premier inda take so a kara adadin 'yan wasan da ake maye gurbinsu yayin wasa daga bakwai zuwa tara har karshen kakar wasa ta bana. (Mail)











